Gwamna Zulum Alheri ne ga al'ummar duniya gaba daya, Sanata Kashim Shettima

Gwamna Zulum Alheri ne ga al'ummar duniya gaba daya, Sanata Kashim Shettima

  • Sanata mai wakiltar Borno ta tsakiya ya jinjinawa Gwamnan jihar bisa rabon kayan da yayiwa al'ummar Gamboru Ngala
  • Shettima ya ce tare da shi aka rabawa mutane sama da dubu sittin kayan abinci da kudi
  • Sanata ya jaddada cewa Gwamna Babagana Umara Zulum na Borno alheri ne ga al'umma

Borno - Tsohon Gwamnan jihar Borno, Kashim Shettima, ya mika godiyarsa ga Gwamna Babagana Umara Zulum, bisa rabon kayan abinci da kudi ga yan gudun hijra a mazabarsa.

Sanata Shettima ya bayyana cewa da kansu suka rabawa mutane sama da dubu sittin kayan abincin cikin kwanaki biyu.

A jawabin da Legit Hausa ta samu daga wajensa, Shettima ya ce Gwamna Zulum alheri ne ga al'umma.

A cewarsa:

"A ranar Lahadi, na raka Gwamna Zulum Gamboru a mota don raba abinci da kudi ga yan gudun hijra inda mukayi kwanaki biyu."

Kara karanta wannan

Yanzu-yanzu: ASUU zata shiga yajin aiki, amma na jan kunne na wata guda

"Da kanmu muka yi rabon kayan abinci da kudi wa mutane 60,813 yan gudun hijra da wadanda aka kawo wajen."
"Gamboru na cikin mazabata kuma muna mika godiya ga wannan kyauta."

Sanata Kashim Shettima
Gwamna Zulum Alherin ne ga al'ummar duniya gaba daya, Sanata Kashim Shettima Hoto: Kashim Shettima
Asali: Facebook

Asali: Legit.ng

Online view pixel