Farfesancin Dakta Pantami: Jami'ar FUTO ta fusata, ta ce ta maka ASUU a kotu
- Jami'ar FUTO a Owerri ta jihar Imo ta ce bata amince da batun ASUU kan Dr Pantami ba, ta ce dole ta tafi kotu a kai
- Wannan na zuwa ne jim kadan bayan da ASUU ta ce sam bata amince da nadin Dr Pantami a matsayin farfesa ba
- Wannan lamari dai na ci gaba da daukar hankulan jama'a a Najeriya, inda wasu ke ganin bai cancanci zama hakan ba
Imo - Shugabar jami’ar tarayya dake Owerri (FUTO), Farfesa Nnenna Oti, ta ce hukumar jami'ar ta garzaya kotu saboda kin amincewa da karin girma da ta yiwa Dakta Isah Ibrahim Pantami a matsayin Farfesa a fannin tsaro na Intanet.
Hakan ya biyo bayan barazanar da kungiyar malaman jami’o’i (ASUU) ta yi na kakabawa FUTO takunkumi kan amincewa da Pantami a matsayin farfesa yayin da yake ci gaba da rike mukami a matsayin minista, inji Daily Nigerian.
Oti ta shaidawa jaridar The Nation jiya Litinin cewa hukumar jami'ar ta garzaya kotu a kan lamarin, inda ta ce duk wani sharhi ko tattaunawa a kai, tozarci ne kawai.
Sai dai wani babban ma’aikacin gudanarwar jami'ar, wanda ya yi magana cikin kwarin giwa, ya yi ikirarin cewa ASUU ba ta da hurumin kutsawa cikin lamarin da ba ta da hurumi akai.
“Kamar yadda ASUU ba za ta gaya wa majalisar jami’ar da kuma majalisar dattawanta wanda ya kamata ta kara wa girma ba, ba kuma za ta gaya musu ka’idojin kara wa wani girma zuwa matakin Farfesa ba.
“A doka, ba za ku iya janye abin da ba ku da shi ba, ASUU ba ita ke tsara nadi da karin girma ba, wasu daga cikin wadannan batutuwa an samo su ne daga ka’idojin NUC, kuma kowace jami’a tana da tsara tsarukanta.”
Ana ci gaba da cece-kuce kan matsayin Dr Pantami na zama farfesa a tun lokacin da aka sanar da ya zama farfesa.
ASUU tace Pantami bai cancanci zama Farfesa ba, zata hukunta FUTO
A tun farko, kungiyar malaman jami'o'i ASUU ta yi watsi da matsayin Farfesa da aka bai wa ministan harkokin sadarwa da tattalin arziƙin zamani, Dakta Isa Pantami.
Punch ta rahoto cewa ƙungiyar bayan taron mambobin majalisar zartarwan ta da ya gudana yau, ta bayyana baiwa Pantami Farfesa a matsayin, "karan tsaye ga doka."
Shugaban ASUU na ƙasa, Farfesa, Emmanuel Osodeke, shi ne ya bayyana haka a wurin taron manema labarai da ƙungiyar ta kira ranar Litinin.
Asali: Legit.ng