Karin bayani: NDLEA ta gano DCP Abba Kyari na safarar kwayoyi tsakanin kasashe
- Hukumar NDLEA ta ce tana neman Abba Kyari ruwa a jallo bayan da ta zarge shi da harkallar miyagun kwayoyi
- Wannan na zuwa ne daidai lokacin da yake gaban hukuma kan zargin hannu a wata harkallar damfara a kasar waje
- Yanzu dai NDLEA ta bayyana dalla-dalla yadda ta gano yana hannu a babbar harkallar miyagun kwayoyi
Abuja Hukumar NDLEA ta ayyana jami'in dan sanda shugaban rundunar IRT da aka dakatar, DCP Abba Kyari cikin wadanda take nema ruwa a jallo bisa zargin safarar miyagun kwayoyi.
Hukumar ta NDLEA ta ce bincike ya nuna cewa jami'an da ya shahara kuma yake karkashin bincike bisa zargin hannu a wata damfara, Kyari mamba ne na wata kungiyar harkallar miyagun kwayoyi da ke hada-hadarta a fadin duniya.
Da dumi: Bidiyon lokacin da Abba Kyari ke bada cin hancin daloli don shigo da hodar Iblis ya bayyana
Kakakin hukumar ya bayyana haka ne a wata zantawa da manema labarai a ranar Litinin, kamar yadda Legit.ng Hausa ta samo daga NDLEA.
A sanarwar da ta iso mu, NDLEA ta ce tana zargin Abba Kyari da yin harkallar hodar iblis da nauyinta ya kai kilo 25.
Hukumar ta kuma nuna damuwa kan cewa, ta yi mamakin yadda wadanda ya kamata su za su tsawatar amma su ake samu dumu-dumu a cikin miyagun laifuka.
Yadda aka gano bakar harkallar Kyari
Da yake jawabi a taron manema labarai, Babafemi ya ce hukumar yaki da fataucin miyagun kwayoyi ta yi imani da cewa:
"DCP Kyari mamba ne na tawagar masu safarar miyagun kwayoyi da ke gudanar da harkallar haramtattun kwayoyi a Brazil-Habasha-Nigeria".
A wani labarin, hukumar hana fasa kwabrin kwayoyi a Najeriya tayi bayani filla-filla yadda ya gano dakataccen DCP na yan sandan, Abba Kyari, yana safarar kwayoyi.
Kakakin NDLEA, Femi Babafemi, a hira da manema labarai a Abuja ranar Litinin, ya ce Abba Kyari mamban kungiyar masu safarar kwayoyi daga Brazil zuwan Habasha zuwa Najeriya.
Babafemi yace Kyari ya tuntunci wani jami'in hukumar a Junairun 2022 da a saki wasu hodar iblis da aka kama.
Asali: Legit.ng