Neja: Mata 3 Sun Haihu a Daji Yayinda Suke Tserewa Daga Harin Da 'Yan Bindiga Suka Kai Garinsu

Neja: Mata 3 Sun Haihu a Daji Yayinda Suke Tserewa Daga Harin Da 'Yan Bindiga Suka Kai Garinsu

  • Mata uku masu juna biyu sun haihu a daji yayin da suke kokarin gudun neman tsira daga farmakin ‘yan bindiga a kauyakun su da ke karkashin karamar hukumar Magama a Jihar Neja
  • An samu bayanai akan yadda farmakin da ‘yan bindigan suka kai garin Mabirni, Zoma, Bado, Yangula, Buga Zabbu da Ataba ya ki tsayawa tun ranar Juma’a har ranar Lahadi da rana kuma suna kokarin afkawa garin Ibeto
  • Babu kataimaiman yawan mutanen da suka halaka ko kuma suka yi garkuwa da su, sannan cikin mata ukun da suka haifi jariran, har yanzu ba a ga daya ba, jaririn kawai aka tsinta

Neja - Mata uku masu juna biyu sun haihu a daji yayin kokarin guduwa daga farmakin da ‘yan bindiga suka kai kauyakun su da ke Karamar Hukumar Magama cikin Jihar Neja.

Kara karanta wannan

Yan bindiga sun shafe tsawon kwanai 3 suna kai mamaya garuruwan wata jiha a arewa

The Nation ta samu bayanai akan yadda tun ranar Juma’a harin ke ta aukuwa har ranar Lahadi da rana babu kakkautawa.

Neja: Mata 3 sun haihu a hanya yayinda suke tserewa daga wasu garuruwan da ‘yan bindiga suka kai hari
Mata 3 sun haihu a hanya yayin tsere wa daga harin 'yan bindiga. Hoto: The Punch
Asali: UGC

Garuruwan da suka afka mawa sun hada da Mabirni, Zoma, Bado, Yangalu, Buga Zabbi da Ataba. Kuma yanzu haka ‘yan bindigan suna dosar garin Ibeto.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Kawo yanzu, ba a san iyakar yawan mutanen da suka halaka ba

Har yanzu ba a san yawan mutanen da suka halaka ba sakamakon harin, sannan ba a san yawa wadanda aka yi garkuwa da su ba.

Mazauna kauyakun suna tsaka da gudu suka tsinci jariri a daji.

The Nation ta tattaro bayanai akan yadda ‘yan bindiga suka harbi wani Alhaji Ibrahim Maiquaqua Yangalo sannan suka sace wasu daga cikin iyalan sa.

Shugaban karamar hukumar Magama, Safiyanu Garba Ibeto ya tabbatar da aukuwar lamarin.

Kara karanta wannan

Yan bindigan sanye da kayan sojojin Najeriya sun bindige wani shahararren dan kasuwa har lahira

Kamar yadda ya ce:

“Yan bindiga sun shiga karamar hukumar Magama ta Mabirni, Zoma, Bado da Yangalu. Yanzu haka suna kusantar Ibeto, don saura kilomita 23 su isa Ibeto.”

Sun fara neman kudin fansa, Naira miliyan uku

Wata dattijuwa, Malama Khadijat Abdullahi, ta bayyana yadda suka sace yaranta biyu, wata mata mai yara biyar da kuma wata mai yara uku.

Ta ce ‘yan bindigan sun fara tuntubar su inda suka bukaci kudin fansa naira miliyan uku.

Yawancin mutanen da suke zama a kauyakun sun tsere a ranar Lahadi da safe, sannan ‘yan bindigan sun ci gaba da satar shanu a wasu kauyakun.

Mazauna kauyakun sun koma Kontogora a matsayin ‘yan gudun hijira.

'Yan bindiga sun afka wa mutane a kan titi a Kaduna, sun kashe shida

A wani labarin, wasu da ake zargin makiyaya fulani ne sun kai wa mutane da ke tafiya a hanya hari a gaban Makarantar Sakandare ta Gwamnati da ke Kagoro, Karamar Hukumar Kaura ta Jihar Kaduna.

Kara karanta wannan

Yan bindiga sun hallaka mutum 10, sun sace Hakimi a jihar Katsina

Wani ganau, wanda ya tabbatar wa The Punch rahoton a ranar Alhamis, ya ce yan bindiga sun taho ne a kan babura sannan suka far wa wadanda suka gani.

Ya ce mutane shida ne aka tabbatar sun rasu sakamakon harin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164