Tashin hankali: Yan bindiga sun sake kashe jami’an yan sanda 4 a Enugu
- Wasu yan bindiga da ba a san ko su wanene ba sun farmaki wasu yan sanda da ke aiki inda suka bindige guda hudu har lahira
- Maharan sun budewa jami'an wuta ne a Amodo Obeagu da ke karamar hukumar Enugu ta kudu a jihar Enugu a ranar Asabar, 12 ga watan Fabrairu
- Harin na zuwa ne kasa da sa’o’i 48 bayan wasu yan bindiga sun harbe jami’an yan sanda uku a jihar
Enugu - Jaridar The Nation ta rahoto cewa wasu yan bindiga da ba a san ko su waye ba sun bindige jami’an yan sanda hudu a Amodo Obeagu da ke karamar hukumar Enugu ta kudu a jihar Enugu.
Lamarin wanda ya afku a yammacin ranar Asabar, 12 ga watan Fabrairu, na zuwa ne kasa da sa’o’i 48 bayan wasu yan bindiga da ba a san ko su waye ba sun harbe jami’an yan sanda uku a Enugun.
An tattaro cewa maharan sun farmaki wani shingen bincike na yan sanda a hanyar Agbani, sannan suka budewa jami’an wuta lamarin da ya yi sanadiyar mutuwar jami’ai hudu a nan take.
An kuma ruwaito cewa wasu jami’ai da suka tsallake rijiya da baya sun jikkata sakamakon harin bindiga kuma cewa harin ya shafe kimanin tsawon mintuna biyar.
Mazauna kauyen sun kuma bayyana cewa maharani sun farmaki shingen binciken yan sanda a Amodo cikin motocin Sienna guda biyu sannan suka yi ta harbi har bayan sun kashe jami’an.
An kuma ce yan bindigar da suka harbe yan sanda a hanyar Timber Road, sun yi garkuwa da wata mata da direbanta.’
Jaridar Premium Times ta rahoto cewa kakakin yan sandan jihar Enugu, Daniel Ndukwe ya tabbatar da harin amma bai bayyana adadin wadanda aka kashe ba.
Sai dai kuma, wata majiya ta yan sanda ta bayyana cewa an kashe yan sanda hudu a Amodo.
Majiyar ta ce:
"Yara maza ne da ke neman bindigu amma za mu sauya dabaru da mayar da hankali wajen gudanar da sintiri a Enugu."
Karin bayani: 'Yan Bindiga Sun Harbe 'Yan Sanda 3 Har Lahira Yayin Da Suke Bakin Aikinsu
A baya mun ji cewa hankula sun tashi a ranar Alhamis a yayin da wasu yan bindiga da ba a san ko su wanene ba suka bindige yan sanda uku har lahira a shingensu a Enugu.
Lamarin ya faru ne a kan timber junction, kusa da Maryland a karamar hukumar Enugu ta kudu kamar yadda Vanguard ta ruwaito.
Vanguard ta gano cewa wani direban Keke Napep ya jikkata sakamakon harsashin da miyagun suke ta harbawa daga bindigansu domin su firgita mutane.
Asali: Legit.ng