Abdulsamad da ɗansa sun samu fiye da N508bn cikin kwana 24, sun shige gaban Ɗangote da sauran biloniyoyi

Abdulsamad da ɗansa sun samu fiye da N508bn cikin kwana 24, sun shige gaban Ɗangote da sauran biloniyoyi

  • Rahotanni sun nuna yadda Abdulsamad Rabiu, shugaban BUA Group da dansa suka zarce Dangote dukiya cikin kwanaki kadan
  • Sun samu wannan tsabar dukiyar ne ta hannayen jarin da suka mallaka a kamfanin BUA wanda darajar sa ta nunku sosai
  • Rabiu da dan sa sun samu fiye da N500b wanda yanzu haka suka zarce wasu jerin biloniyoyi inda suka koma matakin na daya da na biyu

Abdulsamad Rabiu, shugaban kafanin BUA Group da dansa, sun koma saman jerin biloniyoyin Najeriya ‘yan kasuwa a watan Janairu bayan sun samu N508bn wanda N20.3bn ke samuwa a ko wacce rana.

Sun koma saman jerin ne bayan darajar kayan abincin kamfanin BUA ya karu Kasuwan Hannun Jari ta Najeriya da kaso 61% yayin da na simintin BUA ya karu da kaso 5.5% cikin watan.

Kara karanta wannan

Satar Abacha: Najeriya ta dauki Lauya, za tayi shari’a da kasar Birtaniya a kan €180m

Abdulsamad da ɗansa sun samu fiye da N508bn cikin kwana 24, sun shige gaban Ɗangote da sauran biloniyoyi
Abdulsamad da ɗansa sun samu fiye da N508bn cikin kwana 24, sun zarce Ɗangote da sauran biloniyoyin Najeriya. Hoto: BUA
Asali: UGC

Rabiu yana da 16.7bn na hannayen jari daga kamfanin kayan abinci na BUA, inda yake da kaso 89.95% na gabadaya kamfanin. Sannan a kamfanin simintin sa yana da kaso 92.27%, kamar yadda Nairametrics ta ruwaito.

Dansa yana da hannayen jari miliyan 1.79 daga kamfanin kayan abincin BUA, inda yake da kaso 9.96% na kamfanin. Shi da mahaifinsa suna da kaso 99.8% na hannun jarin kamfanin abinci na BUA.

Biloniyoyin da aka samu a cikin ‘yan kasuwa a watan Janairun 2022

Abdulsamad Rabiu ya samu riban N465.1b a watan Janairu zuwa Naira tiriliyan 2.39, yayin da dansa ya zama na biyu a masu riba inda ya samu N43.73b.

Na uku a jerin kuma Jim Ovia ne, wanda ya samu N3.19b a watan Janairu bayan hannun jarin bankin Zenith ya kara kima da kaso 3.6%.

Kara karanta wannan

Jonathan: Asalin abin da ya sa na kirkiro makarantun Almajirai a Arewa a mulkina

Ovia yana da hannayen jari N3.55b kai tsaye na bankin, sai kuma wasu hannayen jari N1.53m a kaikaice, inda ya mallaki kaso 16.16% na bankin, wanda ya zama na hudu a jerin masu kudin Afirka.

Aliko Dangote, wanda yake da hannayen jari N27.64m kai tsaye na kamfanin simintin Dangote, sai kuma hannayen jari 14.62b a kaikaice na kamfanin da sauran kamfanoninsa. Gabadaya yana da kaso 85.97% na kamfanin.

Dangote yana da hannayen jari N673.1m na kamfanin sigar Dangote inda yake da kaso 5.38% na gabadaya kamfanin.

A watan Janairu, Dangote ya samu N7.2b daga kamfanin simintin Dangote yayin da kamfanin sigar Dangote ya samar masa da N11.43bn, idan aka hada ya samu N18.63bn gabadaya

Ana bin kowanne ɗan Najeriya bashin N64,684 bisa basukan da ƙasar ta ci a ƙasashen waje

A wani labarin, kun ji cewa bisa yawan ‘yan Najeriya da kuma yawan basukan da ake bin ta, kowa ya na da N64,684 a kan sa.

Kara karanta wannan

Tarihi a 2022: Manya-manyan laifukan kashe-kashen tsafi 4 da suka girgiza 'yan Najeriya

Kamar yadda kowa ya san yawan bashin da Najeriya take ta amsowa daga kasashen ketare, yanzu ko wanne dan Najeriya ya na da bashin $157 ko kuma N64,684 a kan sa.

Bisa wannan kiyasin, masanin tattalin arzikin kasa, Dr. Tayo Bello ya bayyana damuwar sa akai inda ya ce duk da zuzurutun basukan, babu wasu abubuwan ci gaba da aka samar wadanda za su taimaka wurin biyan basukan kamar yadda Leadership ta ruwaito.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164