Gold Souk: Gwamnatin Buhari za ta karasa kasuwar gwala-gwalai ta Kano kafin karshen 2022
- Gwamnatin shugaban kasa Muhammadu Buhari ta ce za ta karasa kasuwar gwala-gwalai ta Kano kafin karshen 2022
- FG ta ce kasuwar za ta yi gogayya da takwarorinta na duniya da zaran an kammala ta kuma ta fara aiki
- Ministan ma'adinai da karafe, Mista Olamilekan Adegbite, ya bayyana hakan a ranar Laraba, 9 ga watan Fabrairu, a Abuja
Gwamnatin tarayya karkashin jagorancin shugaban kasa Muhammadu Buhari ta bayyana cewar za ta kammala ginin kasuwar gwala-gwalai ta jihar Kano kafin karshen shekarar 2022.
Gwamnatin tarayyar ta bayyana cewa kasuwar gwala-gwalan za ta yi gogayya da sauran kasuwannin gwala-gwalai na duniya idan aka kammala ta kafin karshen shekarar nan.

Source: Facebook
A cewar wata sanarwa da mai ba shugaban kasa shawara a kafofin sadarwa ta zamani, Bashir Ahmed ya fitar a shafinsa na Twitter, ya ce ministan ma'adinai da karafe, Mista Olamilekan Adegbite ne ya bayyana wannan ci gaban.

Kara karanta wannan
Buhari ya bi ayarin malaman addinai, ya hada ASUU da Allah da Annabi kada su tafi yajin aiki
Ya rubuta a shafin nasa:
“Gwamnatin tarayya za ta kammala kasuwar gwala-gwalai ta Kano kafin karshen 2022. Kasuwar gwala-gwalan wacce ake ginawa a jihar Kano, idan aka kammala ta kuma ta fara cikakken aiki za ta yi gogayya da kasuwannin gwala-gwalai da ke sauran yankunan duniya, ministan ma'adinai da karafe ya bayyana haka."
Martanin jama'a kan wannan ci gaban
Mabiya shafin hadimin shugaban kasar sun je bangaren sharhi domin fadin albarkacin bakunansu kan lamarin.
@ibnabubakar1991 ya yi martani:
"Okay, munji! Sai me?"
@Zellencekelly ya ce:
"A matakin da aka kai a rayuwar gwamnatin nan kamata yayi mu dunga jin cewa, mun kammala amma ba wai ace za a kammala ba."
@auwalabdallahh ya yi martani:
"Ana hadawa da insha allah-shawara"
Gwamnatin tarayya ta gano dimbin arzikin gwal a hanyar Abuja zuwa Nasarawa
A wani labari na daban, ministan ma'adinai da karafuna, Olamilekan Adegbite, ya cewa gwamnatin tarayya ta gano dimbin arzikin gwal a hanyar Abuja zuwa Nasarawa.
Ministan ya bayyana hakan yayinda ya kaiwa gwamnan jihar, Abdullahi Sule, ziyara ranar Talata.
Adegbite yace an gano arzikin gwal din ne lokacin wani aikin hakan ma'adinai a hanyar.
"Mun yi irin wannan bincike a fadin kasar nan kuma mun gano dimbin arzikin gwal musamman iyakan Abuja zuwa Nasarawa," yace.
Asali: Legit.ng
