Gwamnatin tarayya ta gano dimbin arzikin gwal a hanyar Abuja zuwa Nasarawa

Gwamnatin tarayya ta gano dimbin arzikin gwal a hanyar Abuja zuwa Nasarawa

- Kamar Zamfara, akwai dimbin arzikin gwal a hanyar Abuja zuwa Nasarawa

- Gwamnan Nasarawa ya bayyana cewa ai tuni wasu na haka ba bisa doka ba

- Ana tsoron abinda ya faru a Zamfara na iya faruwa a Nasarawa

Ministan ma'adinai da karafuna, Olamilekan Adegbite, ya cewa gwamnatin tarayya ta gano dimbin arzikin gwal a hanyar Abuja zuwa Nasarawa.

Ministan ya bayyana hakan yayinda ya kaiwa gwamnan jihar, Abdullahi Sule, ziyara ranar Talata.

Adegbite yace an gano arzikin gwal din ne lokacin wani aikin hakan ma'adinai a hanyar.

"Mun yi irin wannan bincike a fadin kasar nan kuma mun gano dimbin arzikin gwal musamman iyakan Abuja zuwa Nasarawa," yace.

Adegbite ya ce ma'aikatarsa ta kaddamar da shirin hakan ma'adinan ne kuma an zuba kudi N15bn ciki.

Ya kara da cewa wannan shiri ya janyo hankulan masu sanya hannun jari kan hakar ma'adinai a Najeriya.

KU KARANTA: Kungiyar Ibo ta buƙaci a kama Sheikh Ahmad Gumi a bincike shi

Gwamnatin tarayya ta gano dimbin arzikin gwal a hanyar Abuja zuwa Nasarawa
Gwamnatin tarayya ta gano dimbin arzikin gwal a hanyar Abuja zuwa Nasarawa
Asali: Depositphotos

DUBA NAN: Buhari ya bada umurnin a bindige duk wanda aka gani da AK-47

A jawabin gwamnan Nasarawa Abdullahi Sule, ya yi alhinin yadda ake hakan arzikin gwal a jihar ba bisa doka ba.

Ya ce jihar shirye take da aiki tare da ma'aikatar wajen kawo karshen haka.

Martani kan hakan, Minista Adegbite ya ce ma'aikatarsa na aiki tare da jami'an tsaro domin tabbatar da cewa abinda ke faruwa a Zamfara ya maimaita kansa a Nasarawa.

A ranar 2 ga Maris, shugaba Muhammadu Buhari ya haramtawa jirage bin sararin samaniyar jihar Zamfara, biyo bayan sace daliban yan makarantar sakandare a jihar.

Hakazalika, shugaban ya haramta ayyukan hakan ma'adinai ga kamfanoni masu zaman kansu.

Ya dau wadannan matakai ne don dakile matsalar tsaro a jihar,

Rashidah Abdul Rahman 'yar jarida ce kuma dalibar ilimi wacce ta kwashe shekaru kimanin uku yanzu tare da shararriyar jarida Legit.

Ta samu gogewa a ɓangaren rubutun labarai akan fannoni shatta, wanda suka hada da siyasa, kasuwanci, wasanni, nishadi, dss.

Asali: Legit.ng

Online view pixel