Zakzaky ya gurgunce, matarsa ta sukurkuce: Kungiya ta roki Buhari da ya basu damar fita kasar
- Wata kungiyar kare hakkin bil Adama, ta yi kira ga shugaba Buhari da ya duba lamarin shugaban kungiyar IMN da matsar Zeenatuddin
- A cewar kungiyar, a halin yanzu Sheikh Zakzaky ya gurgunce kuma matarsa Zeenatuddin ta sukurkuce don ko tafiya ba ta iyawa
- Ya bukaci gwamnatin Buhari da ta saka baki a sakar musu fasfotinsu domin su fice daga kasar nan su nemo lafiyarsu
Wata kungiya mai rajin kare hakkin bil'adama ta sanar da rashin lafiyar shugaban kungiyar shi'a ta Najeriya, Sheikh Ibrahim Zakzaky da matarsa Zeenatuddin, inda suka ce a halin yanzu Zakzaky ya gurgunce, yayin da matarsa ke amfani da kujerar guragu.
A wata takarda da sakataren watsa labaran kungiyar, Mr Segun Fanimo ya sa hannu a ranar Alhamis a Kaduna, kungiyar ta shawarci gwamnatin shugaban kasa Muhammadu Buhari da ta jikan bil'adama, Daily Trust ta ruwaito hakan.
Daily Trust ta ruwaito cewa, ta saki takardun tafiyar Zakzaky da matarsa, wadanda babbar kotun shari'a ta sallame su bayan ta gano basu da laifi, don neman lafiyar su "saboda irin mummunan halin da Najeriya ta saka su."
Kamar yadda takardar ta zo, "Ko shugaban kasa Muhammadu Buhari ya na samun lokacin hutu daga aiki don neman lafiyar sa a kasar waje, saboda haka, ba adalci bane a hana shugaban 'yan shi'an damar zuwa kowacce kasa neman lafiyar sa da ta tabarbare.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
"Sannin kan ka ne, kotun shari'a ta jihar Kaduna ta fi wata shida da sallama gami da wanke shugaban kungiyar Musuluncin, Sheik Ibrahim Zakzaky da matar sa daga laifin da aka zarge su da shi a baya, bayan tsare su da aka yi na kusan shekara shida.
"An kama mata da mijin tun watan Disamba 2015, wadanda suke tsare a hannun DSS, kafin a mika su gidan gyaran hali a jihar Kaduna, a yanayin rashin imani da kaskanci.
"Ba su samun cikakkiyar kulawa, hakan ya zamo barazana ga rayuwar su, duba da irin raunikan da harsasai suka yi musu da tarin matsalolin lafiya, wanda yake bukatar a maida hankali a kai; a saboda haka ne lafiyar su ta ke cigaba da tabarbare wa a kullum."
Ya kara da cewa:
"Bayanan da muke da su, sun nuna yadda lafiyar su ke cigaba da munana, kamar yadda aka ga babban malamin a gurgunce, ita kuma matarsa Zeenatuddin Ibrahim a kan kujerar guragu.
"Muna kira ga shugaban kasa Muhammadu Buhari da antoni janar na tarayya da su saki takardun tafiyar Sheikh da matarsa domin samun cikakkiyar kulawa a kasar waje."
Bayan kamuwa da corona: IMN na so a gaggauta sakin Sheikh Zakzaky da matarsa
Ku nemi kujerun sanatoci, ku bar matasa su shugabanci kasar - Tsohon ministan Buhari ga Atiku da Tinubu
A wani labari na daban, kungiyar yan uwa Musulmai na Shi’a wacce aka fi sani da Shi’a sun nuna damuwar cewa bayan kwanaki shida da kamuwa da annobar korona a kulle, ba a kai Malama Zeenah Ibrahim, matar Sheikh Zakzaky zuwa kowani asibiti na musamman don samun kulawar likita ba.
A wani jawabi daga Shugaban kungiyar, Ibrahim Musa a ranar Juma’a, 22 ga watan Janairu, kungiyar ta nuna tsoron cewa cutar na iya zama barazana ga rayuwar matar don haka suke kira ga sakinta cikin gaggawa, Daily Trust ta ruwaito.
Asali: Legit.ng