Bayan kamuwa da corona: IMN na so a gaggauta sakin Sheikh Zakzaky da matarsa

Bayan kamuwa da corona: IMN na so a gaggauta sakin Sheikh Zakzaky da matarsa

- Kungiyar IMN ta nemi gwamnatin tarayya ta gaggauta sakin shugabansu, Sheikh Zakzaky da matarsa Malama Zeenat

- IMN ta ce matar shugaban nasu na bukatar samun kulawar likita saboda kamuwa da tayi da cutar korona

- Sun ce rayuwarta na cikin hatsari kasancewar tana dauke da wasu lalurori ga kuma yawan shekaru da suka ja

Kungiyar yan uwa Musulmai na Shi’a wacce aka fi sani da Shi’a sun nuna damuwar cewa bayan kwanaki shida da kamuwa da annobar korona a kulle, ba a kai Malama Zeenah Ibrahim, matar Sheikh Zakzaky zuwa kowani asibiti na musamman don samun kulawar likita ba.

A wani jawabi daga Shugaban kungiyar, Ibrahim Musa a ranar Juma’a, 22 ga watan Janairu, kungiyar ta nuna tsoron cewa cutar na iya zama barazana ga rayuwar matar don haka suke kira ga sakinta cikin gaggawa, Daily Trust ta ruwaito.

KU KARANTA KUMA: Da’awar zaman lafiya: Malaman Kirista na arewa sun jinjinawa Sheikh Gumi

Bayan kamuwa da corona: IMN na so a gaggauta sakin Sheikh Zakzaky da matarsa
Bayan kamuwa da corona: IMN na so a gaggauta sakin Sheikh Zakzaky da matarsa Hoto: Sahara Reporters
Asali: UGC

Jawabin ya zo kamar haka:

“Duk mun san cewa annobar korona na bukatar kulawar gaggawa, kuma ma, an hana Malama Zeenah Ibrahim samun kulawar likitoci ciki harda ciwon gwiwa mai tsanani na tsawon shekaru biyar yanzu. Duk da haka tana nan a kurkukun Kaduna a halin yanzu, ba a kwantar da ita a asibiti ba, kuma har yanzu ba ta samu kulawar lafiyar da ta dace ba.

“Idan aka yi la’akari da lalura ta rashin lafiya da take ciki da kuma shekaru da suka ja, cutar zai sanya ta cikin hatsari sosai na mummunan rashin lafiya ko mutuwa. Sheikh Zakzaky da kansa yana fama da lalura da yawa wadanda za su sanya shi cikin hatsari idan har ya kamu da alamomin cutar mai barazana ga rayuwa.

“Ma'auratan suna gab da bayyana a gaban kotu ranar Litinin 25 ga Janairu don fuskantar tuhumar karya da gwamnatin El-rufa’i ta gabatar a kansu. Tsawon lokacin da suka kwashe a tsare tun lokacin da aka kamasu a shekarar 2015 ya karfafa ra'ayin cewa gwamnatin Buhari na mayyar farautar ma’auratan tare da cin zarafin tsarin shari'a da fatan cewa za su mutu cikin sirri a tsare.

“Mun yi imanin cewa bai kamata a tsare Sheikh Zakzaky da matarsa ba tun farko. Wata kotu mai inganci a Abuja ta 'yanta su duka a ranar 2 ga watan Disamba, 2016 amma gwamnatin tarayya ta ki bin umarnin kotun.

“Muna kira ga‘ yan Najeriya masu fada aji da kuma al’ummar duniya da su yi nasara a kan Gwamnatin Tarayya da ta Jihar Kaduna don tabbatar da kula da lafiyar wannan mara lafiyar da ke cikin shekarunta na 60 kuma har yanzu tana cikin alhinin kisan da aka yi wa ’ya’yanta 6. Muna rokon Allah Madaukakin Sarki da Ya ba ta lafiya, Ya tsare mijinta da sauran fursunoni har da jami’an gidan yarin daga wannan mummunar cutar.”

KU KARANTA KUMA: Dakarun rundunar sojin Najeriya sun ragargaji yan Boko Haram, sun kashe mutum 5

A baya mun ji cewa Uwargidar shugaban kungiyar mabiya akidar Shi'a a Najeriya, Hajiya Zeenatu Zakzaky, ta kamu da cutar Coronavirus, an samu labari ranar Alhamis.

'Dan El-Zakzaky, Mohammed, ya tabbatar da halin da mahaifiyarsa ke ciki a jawabin da ya baiwa manema labarai.

Kusan makonni biyu a jere, yan Najeriya sama da 1000 ke kamuwa da Korona kullum.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel