Tirkashi: An gano zunzurutun dukiyar da Cristiano Ronaldo ke samu a duk wallafarsa ta Instagram

Tirkashi: An gano zunzurutun dukiyar da Cristiano Ronaldo ke samu a duk wallafarsa ta Instagram

  • Dan wasan kwallon kafa wanda ya shahara a duniya, Cristiano Ronaldo, ya na samun kudi da suka kai £1.7 miliyan a kowacce wallafarsa ta Instagram
  • An gano cewa, Ronaldo ne dan Adam da aka fi bibiyar shafinsa a kafar sada zumunta ta Instagram kuma ya na samun kudi fiye da na kwallonsa
  • Kungiyar Manchester United ta na biyan zakaran dan kwallon kafan kudi da ya kai £480 a kowanne mako, amma na Instagram ya ninka sau uku

Fitaccen dan wasan kwallon kafa na duniya, Cristiano Ronaldo, mai mabiya sama da miliyan dari hudu shi ne dan Adam da jama'a suka fi bibiyar shafinsa na Instagram a duniya.

An gano cewa irin makuden kudaden da ya ke samu a duk wallafar da yayi sun kai £1.7 miliyan, shafin Linda Ikeji ya ruwaito.

Kara karanta wannan

Ronaldo, Ozil, Mane da sauran ‘Yan kwallon kafa da suka fi kowa taimakawa marasa karfi

Dan wasan kwallon kafan kungiyar kwallo ta Manchester United din ya zama wanda jama'a suka fi bibiyar shafinsa na Instagram a ranar Asabar da ta gabata, inda Kylie Jenner ke biye da shi a matsayi na biyu.

Tirkashi: An gano zunzurutun dukiyar da Cristiano Ronaldo ke samu a duk wallafarsa ta Instagram
Tirkashi: An gano zunzurutun dukiyar da Cristiano Ronaldo ke samu a duk wallafarsa ta Instagram. Hoto daga @cristiano
Asali: Instagram

A halin yanzu, kwararru a fannin caca, OLBG sun ce Ronaldo ya na samun kudin da ya kai fam 1.77 miliyan a duk wallafar da yayi a shafinsa saboda a kalla mutum miliyan goma ke duba wallafar.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

A watan Satumbar shekarar da ta gabata, Ronaldo ya na da mabiya da suka kai 237 miliyan wanda hakan yasa ya ke samun makuden kudin da suka kai £1,019,100 a kowacce wallafa.

Da wadannan mabiyan dubu dari hudu da daya, samun Ronaldo ya kai £1,720,000 rubi uku na £480k da ya ke samu a kowanne mako daga kungiyar kwallon kafa ta Manchester United.

Kara karanta wannan

Cikin sauki: Yadda wani mutum ya yi biki mai kayatarwa, ya kashe N20,500 kacal

Wannan yawan mabiyan da ya ke da su ya nuna cewa jimillar mabiyansa sun wuce dukkan yawan mabiyan kungiyoyin kwallon kafa na Turai 92.

Aljannar duniya: Hotunan cikin katafarun gidajen £45m na Ronaldo da motocin alfarma

A wani labari na daban, fitaccen dan wasan kwallon kafa a duniya, Cristiano Ronaldo, mutum ne mai son shakawata da fantamawa a cikin dukiyarsa.

Kamar yadda UK Sun ta wallafa, Ronaldo ya na da gidaje da motoci masu darajar sama da £45 miliyan, daga katafaren gidan na Madeira mai darajar £7 miliyan zuwa motarsa kirar Bugatti mai darajar £8.5 miliyan har kan marsandin sa mai darajar £14,000.

Ronaldo na iya barin gidansa na Cheshire zuwa wadannan gidajen, uku kacal daga cikin katafarun gidajensu masu darajar sama da £23 miliyan.

Ana bayyana cewa ya mallaki motoci kirar Bugatti tare da wata La Voiture Noire mai darajar £8.5 wacce guda goma kacal aka kera.

Kara karanta wannan

Wadanda suka sace yan uwan malamin jami’ar Zamfara sun nemi a biya miliyan N70

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Khalid avatar

Aisha Khalid (Hausa editor) Aisha Khalid marubuciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018. Ta kwashe shekaru tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu. Za a iya tuntubar ta a adireshin email din ta kamar haka: aisha.khaleed@corp.legit.ng