Jama’a sun tsere daga gidajensu yayin da yan bindiga suka farmaki garuruwan Neja

Jama’a sun tsere daga gidajensu yayin da yan bindiga suka farmaki garuruwan Neja

  • Jama'a sun gudu sun bar gidajensu a garuruwa biyar a hanyar Kontagora-Rijau da ke kananan hukumomin Mariga da Rijau na jihar Neja saboda hare-haren yan bindiga
  • Maharan dai sun farmaki kauyen Dusai, wanda ke yan kilomita kadan daga garin Kontagora a ranar Lahadi, 6 ga watan Fabrairu
  • Sannan a ranar Litinin, 7 ga watan Fabrairu, sai suka kai hari kauyen Kuimo wanda ke kusa da garin Rijau

Mazauna garuruwa biyar a hanyar Kontagora-Rijau da ke kananan hukumomin Mariga da Rijau na jihar Neja sun tsere sun bar gidajensu sakamakon hare-haren ta’addanci.

Yan ta’addan sun fara kai hari kauyen Dusai, wanda ke yan kilomita kadan daga garin Kontagora a ranar Lahadi, 6 ga watan Fabrairu.

Hakazalika, maharan sun farmaki kauyen Kuimo wanda ke kusa da garin Rijau da misalin karfe 4:00 na ranar Litinin, 7 ga watan Fabrairu.

Kara karanta wannan

Ku sakan mana mazajenmu, Iyalan yan BDC da ake zargi da turawa yan Boko Haram kudi a Kano

Jama’a sun tsere daga gidajensu yayin da yan bindiga suka farmaki garuruwan Neja
Jama’a sun tsere daga gidajensu yayin da yan bindiga suka farmaki garuruwan Neja Hoto: Channels TV
Asali: UGC

Shugaban karamar hukumar Rijau, Bello Bako, wanda ya tabbatar da harin a wata hira ta wayar tarho a ranar Talata, 8 ga watan Fabrairu, ya bayyana cewa babu wanda aka kashe a harin inda ya ce mazauna yankin da dama sun jikkata.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Ya ce:

“Ba mu gani ko mun ji labarin mutuwar wani ba amma mutane da dama sun ji rauni a kokarinsu na tserewa harin yan ta’addan.”

Bako ya kara da cewa shi da jami’ansa suna aiki don tabbatar da ganin cewa wadanda suka tsere sun samu wajen da za su zauna.

Fal’ai Danladi, wacce ta kasance cikin wadanda suka tsere daga harin, ta ce ta ji rauni a lokacin da ta fadi yayin guduwa.

Wani mazauni da ya tsere daga garin Warare, Aliyu Bello, ya bayyana cewa ya yanke shawarar guduwa saboda ya san cewa idan aka sace shi, ba zai ji da dadi ba.

Kara karanta wannan

An kashe jami’an yan sanda uku, an sace mazauna da dama yayin da yan bindiga suka kai hari a Neja

Ya ce:

“Dole na gudu don tsira da raina saboda idan wadannan mutane suka sace ni, ba za mu ji ta dadi ba daga ni har yaun uwana.”

Bello ta ci gaba da bayyana cewa sun bar garinsu sannan suka koma Rijau don samun mafaka.

Niger: 'Yan kauye ne ke bai wa 'yan ta'adda bayanan sirri, Sanata Musa

A gefe guda, Sanata Sani Musa, mai wakiltar gabashin jihar Niger inda 'yan bindiga suke cin karen su babu babbaka, ya yi kira ga mazauna kauyuka da matasa da su hada kawuna don ganin an zakulo gami da wartakar 'yan bindiga a jihar Niger.

Ya kara da kira ga jami'an tsaron da su yi amfani da dabarbarun zamani wajen ganin sun yi gaba da gaba da 'yan ta'addan kamar yadda ya roki gwamnatin tarayya da ta samar da tabbataccen sansanin sojoji a yankunan da ake yawan kai hari, Vanguard ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Da dumi: Yan bindiga sun kashe Hakimi da wasu jama'arsa a jihar Katsina

Sanatan, yayin wata tattaunawar waya da jaridar Vanguard, ya sanar da yadda wasu al'amura marasa dadi suke faruwa a jihar, inda suke nuna yadda wasu 'yan kauye suke da hannu dumu-dumu a ta'addanci, har wasu suke zama 'yan leken asirin 'yan bindigan wanda hakan ke matukar wahalar da jami'an tsaro don ganin sun sheke su.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng