Baba-Saliu: 'Yan bindiga sun sace shugaban IPMAN, sun bindige direbansa har lahira
- Wasu miyagun yan bindiga sun kutsa gidan shugaban kungiyar dillalan man fetur masu zaman kansu ta Najeriya, IPMAN, ta Jihar Edo, Abdullahi Baba-Saliu
- Sun sace Baba-Saliu da karfi da yaji sannan suka bindige daya daga cikin direbobinsa har lahira kana suka jikkata masu tsaronsa da dayan direbansa
- Rundunar yan sandan Jihar Edo ta bakin kakakinta Bello Kotongs ta tabbatar da afkuwar lamarin ta kuma ce suna kokarin ceto wanda aka sace din
Jihar Edo - Yan bindiga sun sace shugaban kungiyar dillalan man fetur masu zaman kansu ta Najeriya, IPMAN, reshen Jihar Edo, Abdullahi Baba-Saliu.
An kashe direbansa da masu gadinsa yayin harin da aka kai gidansa da ke Jattu, Karamar Hukumar Etsako West a Jihar Edo, The Punch ta ruwaito.
Lamarin ya faru ne a daren ranar Litinin, kamar yadda rahotanni suka nuna.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Surukin Baba-Saliu ya tabbatar da afkuwar lamarin
Wani shahararren mai kare hakkin bil adama a Abuja, Abdul Mahmud, wanda suruki ne ga Baba-Saliu ya shaida wa The Punch cewa har yanzu yan bindigan ba su tutubi iyalansa ba.
Ya ce:
"A daren jiya misalin kare 6.45 na yamma, yan bindiga sun sace suruki na, Abdulhamid Baba-Saliu, da karfi da yaji bayan sun kutsa gidansa a garinsu na Jattu, karamar hukumar Esako ta Yamma.
"Yana zaune ne a Benin, Abuja da Jattu inda ya ke da gidajen man fetur, Baba Petroluem. Ya tafi gida ne domin hallartar addu'ar ranar uku na rasuwar kawunsa a makon da ta gabata.
"An kashe daya daga cikin direbobinsa bayan harbinsa da bindiga; dayan direban da kuma masu tsaronsa duk sun samu munanan raunuka. Masu garkuwa da mutanen sun tafi da suruki na. Ba su tuntubi kowa ba, ba su nemi kudin fansa ba a yanzu.
"Muna cikin mawuyacin hali a yanzu. Yayin da muke cigaba da addu'a, ina rokon wadanda suka dauke shi da masu rike da shi su sake shi ya dawo wurin iyalansa da mutanensa na Jattu, Uzairue da ya ke matukar kauna ba tare da taba lafiyarsa ba."
Yan sanda sun bazama domin ceto Baba-Saliu
Mai magana da yawun rundunar yan sandan Jihar Edo, Bello Kotongs ya tabbatar da afkuwar lamarin.
Ya kara da cewa yan sanda suna iya kokarinsu domin ganin sun ceto shi.
'Yan bindiga sun sace mutane 29 a wani ƙauyen Katsina, 'Yan Sanda
A wani rahoton, kun ji cewa mutane 29 ne yan bindiga suka sace yayin harin da suka kai kauyen Godiya a cewar rundunar yan sandan Jihar Katsina.
Mai magana da yawun rundunar a jihar, Gambo Isah, ya tabbatar da adadin mutanen yayin zantawa da Channels Television a ranar Talata.
Wasu gungun yan bindiga ne suka kai hari a Ruwan-Godiya a daren ranar Lahadi a karamar hukumar Faskari.
Asali: Legit.ng