Kaduna: Jami'an tsaro sun ragargaji 'yan bindiga, sun kubutar da wadanda aka sace

Kaduna: Jami'an tsaro sun ragargaji 'yan bindiga, sun kubutar da wadanda aka sace

  • Gwamnatin jihar Kaduna ta tabbatar da sakin wasu mutanen da 'yan bindiga suka sace a wani yankin jihar
  • Wannan na zuwa ne daga bakin kwamishinan harkokin tsaron cikin Samuel Aruwan, a cikin wata sanarwa da ya fitar
  • Gwamnati ta yabawa sojoji da sauran jami'an tsaron da ke kokarin tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a jihar

Jihar Kaduna - Jami’an tsaro sun kubutar da wasu mutane bakwai da aka yi garkuwa da su daga hannun ‘yan bindiga da suka kai farmaki Ungwan Garama, da ke yankin Maraban Rido Janar na karamar hukumar Chikun a jihar Kaduna.

An tattaro daga majiyoyi cewa an samu kiran aukuwar tashin hankali daga yankin inda jami’an tsaro suka yi gaggawar kai daukin dakile ‘yan bindigan, Daily Trust ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Nasara: Yan bindiga sun kwashi kashin su a hannu yayin da suka kai hari Ofishin yan sandan Kogi

Samuel Aruwan, kwamishina tsaron cikin gida a Kaduna
Da duminsa: Jami'an tsaro sun kubutar da wadanda aka sace a jihar Kaduna | Hoto: dailytrust.com
Asali: UGC

Samuel Aruwan, kwamishinan tsaro na cikin gida a jihar Kaduna ne ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da ya fitar, ya ce karfin wutar da sojojin suka yi ya tilasta wa 'yan ta'addan tserewa.

Ya bayyana cewa jami’an tsaro sun tarwatsa hanyar tserewar ta ‘yan bindiga, kuma sun samu nasarar kubutar da mutane bakwai da aka yi garkuwa da su.

Aruwan ya ce dukkan wadanda aka ceto sun koma ga iyalansu lafiya, inda ya ce Gwamna Nasir El-Rufa’i ya yabawa jami’an tsaro bisa irin namijin kokarin da suka yi da kuma saurin daukar matakin.

Gwamnan ya mika gaisuwarsa da fatan alheri ga wadanda aka ceto.

Zamfara: 'Yan ta'adda sun sheke liman, wasu 32, sun sace mata da yara kan kin biyan N40m haraji

'Yan bindiga sun halaka sama da rayuka talatin, sun yi garkuwa da wasu mata a hari mabanbanta a ranar Juma'a duka a jihar Zamfara, Daily Trust ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Rashin tsaro: Gwamnatin Niger ta saka dokar hana fita a kananan hukumomi 2

Yankunan da aka kai farmakin sun hada da Nasarawar mai Fara da ke karamar hukumar Tsafe, Yar Katsina a karamar hukumar Bungudu da kauyen Nasarawa da ka karamar hukumar Bakura.

Zamfara kamar sauran jihohin arewa maso yamma, ta na fama da rashin tsaro. Al'amuran 'yan bindigan kullum kara kamari su ke yi.

Dubban jama'a aka kashe kuma 'yan bindigan sun yi garkuwa da mutane masu yawa a yankin, lamarin da ya kara gaba har jihar Niger tun shekarar 2021.

Zamfara: Sojoji da 'yan sanda sun ceto mutum 32 da 'yan ta'adda suka yi garkuwa da su

A wani labari na daban, rundunar hadin guiwan sojoji da 'yan sanda ta ceto mutane 32 da aka yi garkuwa da su daga bangarori daban-daban na jihar Zamfara.

Yayin zantawa da manema labarai a hedkwatar su da ke Gusau, Muhammad Shehu, mai magana da yawun yan sandan jihar Zamfara, ya ce wadanda aka ceto 'yan jihohin Neja, Katsina da Zamfara ne.

Kara karanta wannan

Tubabbun 'yan Boko Haram na taimakawa wurin yaki da ta'addanci, Zulum

Shehu ya ce: "An kula da wadanda aka ceton yadda ya dace inda 'yan sanda suka musu tambayoyi sannan aka mika su ga iyalan su."

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.