Saura kiris cutar korona ta kai ni lahira, Ministan Buhari ya sanar da gwagwarmayarsa da jinya
- Ministan birnin tarayya Malam Muhammad Musa Bello ya bayyana yadda ya tsallake rijiya da baya sanadiyyar annobar cutar korona
- An killa ce shi na tsawon mako uku bayan da aka yi mishi gwajen cutar Korona a karshen shekarar da ta gabata
- A tsawon mako ukun da yayi jinyar cutar, ba ya samun damar aiwatar da al'amuran rayuwarsa, yayin da har yanzu bai gama dawowa daidai ba
FCT, Abuja - Ministan birnin tarayya, Malam Muhammad Musa Bello ya bayyana yadda ya kusa rasa rayuwar sa sanadiyyar annobar korona lokacin da aka killace shi na tsawon mako uku bayan an yi masa gwajin cutar an gano ya na dauke da ita a karshen shekarar da ta gabata.
Ya bada labarin irin wahalar da ya sha a karshen satin, bayan an mishi riga kafin cutar korona.
Jaridar ThisDay ta ruwaito cewa, ministan ya ce dalilin da yasa ya tsira daga annoban shi ne saboda an yi mishi allurar riga kafin sau biyu.
"Duk da asibiti ba su kwantar da ni ba, an killa ce ni na tsawon mako uku a gida na saboda bayan na gama shan magunguna, an gano ina dauke da cutar bayan an gwada ni sau biyu. Sakamakon gwajin na ukun ya nuna ba na dauke da cutar. Da ace banyi riga kafin cutar har sau biyu ba, da kila abin da ya faru da mutane da yawa, da shi zai faru dani," a yadda ya ce.
Ministan ya bada labarin yadda yayi fama da matsanancin ciwon kai, mura, ciwon gabbai da kasala, yayin da yayi fama da cutar, hakan ya tilasta canza magungunan shi bayan kwana goman farko.
"A tsawon mako ukun, ba na iya hassala komai. Ban fita daga gida ba, ban samu damar aiwatar da al'amura na ba, yayin da har yanzu ban gama dawowa daidai ba, ina dai karfin hali ne don ganin na gama da takardun da ban duba ba lokacin da ina killace," a cewarsa.
Ya bukaci duk mazaunan FCT su yi riga kafin, inda yake shawartar wadanda suka yi na farko da na biyu da su kara yi. Ministan ya ce zai yi kokarin yin abun da ya dace, "saboda ba na fatan kara fuskantar abinda na fuskanta a baya".
Ya yi godiya ga gwamnatin tarayya na ganin ta samar da allurar riga kafin ga 'yan Najeriya, inda ya bukaci mazauna su yi riga kafin domin yin hakan ya na kubutar da rayuka, ThisDay ta ruwaito.
Haka zalika, sakataran kula da harkar lafiya da bukatun dan adam na birnin tarayyar Abuja (FCTA), Dr Abubakar Tafida ya bayyana yadda jimillar mutanen da suka yi riga kafin farko a FCT suka kai 433,000, inda mutane 286,000 ne suka yi rigi kafi na biyu. Kuma kimanin mutane 12,000 sun yi na ukun.
An kuma: Ministan Buhari ya kama da annobar Korona bayan wasan buya da cutar
A wani labari na daban, babban ministan birnin tarayya, Malam Muhammad Musa Bello ya kamu da cutar korona. Ministan ne ya bayyana hakan a shafinsa na Facebook a ranar Juma’a, 31 ga watan Disamba.
Ya ce: “Na kamu da cutar korona. Bayan tsawon watanni 21 (shekara daya da wata 9) muna wasan buya tsakanina da korona, a karshe cutar ta kama ni a ranakun karshe na 2021. Bayan jin zazzabi daga ranar 28 ga watan Disamba, sai na yanke shawarar yin gwajin Covid-19 a safiyar jiya."
Asali: Legit.ng