Dalibin Bethel ya ce ba zai dawo gida ba, 'yan bindiga na gwangwaje shi da ababen duniya
- Dalibin da shi kadai ya rage hannun 'yan bindiga dan makarantar Bethel Baptist ya yi mirsisi ya ki dawowa gida inda ya zabi zama da 'yan bindigan
- An gano yadda 'yan bindigan suke gwangwaje shi da ababen more rayuwa a duk lokacin da suka dawo daga harkallar su
- Hakan ya sa ya yi watsi da tayin da aka yi masa na samun yancin sa inda suka yi garkuwa da wanda ya kai kudin fansar sa
Kaduna - Dalibin da shi kadai ya rage hannun masu garkuwa da mutane dan makarantar Bethel Baptist, ya yi mursisi ya ki dawowa gida, inda ya bayyana yadda yake jin dadin zama da 'yan ta'addan.
Sai dai, 'yan bindigan sun damke mamban kungiyar kiristocin Najeriya (CAN), wanda ya kai kudin fansar da 'yan ta'addan suka bukata bayan ya kai musu sakon, Vanguard ta ruwaito.
Shugaban kungiyar kiristocin Najeriya (CAN) a jihar Kaduna, Rev Joseph John Hajab, da mataimakin kungiyar a arewa, sun nuna damuwar su saboda ganin yadda "Dalibin da shi kadai ya rage, kuma mafi kankanta daga cikin wadanda aka yi garkuwa da su, yayi watsi da tayin da aka yi masa na samun 'yanci daga hannun yan ta'addan."
Idan za'a tuna, an yi garkuwa da dalibai 121 na makarantar Bethel Baptist a 5 ga watan Julin 2021 a harabar makarantar da ke kan titin Kaduna zuwa Kachia a Dishi a karamar hukumar Chikun da ke jihar Kaduna, amma daga bisani aka saki guda 120.
"Dalibin da ya ragen ya zabi ya zauna da 'yan bindigan, hakan ya matukar ba dukkan mambobin Baptist da gaba daya kungiyar CAN mamaki. An gano yadda 'yan bindigan suke gwangwaje shi da ababen duniya a duk lokacin da suka dawo daga harkallar su, hakan yasa yayi watsi da tayin 'yancin da aka mishi," a cewar Hayab.
"A tunani na masu garkuwa da mutanen suna da matukar wayau. Sun yi kokarin canza masa ra'ayi har ya iya cewa ya zabi zama da su. Suna bashi nama, da ababen more rayuwa a duk lokacin da suka fita suka dawo, sun fifita shi a kan sauran, inda suke ba shi abubuwa da dama, shiyasa ya canza gaba daya."
Ya kara da cewa:
"Idan suka ce ya tafi gida, sai ya ce ba zai je ba, har ya na kawo wasu dalilan da ba su taka kara sun karya ba na cewa iyayen shi suna dukan shi a gida. Amma mun bincika mun gano gaskiya, ba ma so mu fallasa iyayen sa ga wani hayaniya, amma haka ya fadi. Muma mun kasa ganewa.
"Sai dai na fahimci yadda suke wasa da kwakwalwar sa ta hanyar bashi kyaututtuka har suka gamsar da shi yake magana haka. Amma wancan satin da ya gabata, sun ce mana mu kawo kudi mu amshe shi.
"Wanda ya kai kudin shima sun yi garkuwa da shi. Ya na hannun su yanzu haka da nake magana.
"Saboda haka, al'amarin akwai rudani shiyasa muke taka tsan-tsan. Mutumin da yake taimaka mana gurin kai kudin duk tsawon lokacin nan don ganin an saki yaron da suke hargitsa wa tunani, shi ma sun yi garkuwa da shi. Yanzu duk al'amarin babu fasali, dole mu kula."
Vanguard ta ruwaito cewa, Hayab ya kara kira ga hukumomi da su taimaka don ganin an saki sauran wadanda aka yi garkuwa da su a jihar.
Yan bindiga sun sako karin dalibai 10 cikin yan makarantar Bethel Baptist a Kaduna
A wani labari na daban, a kalla karin daliban makarantar Bethel Baptist College dake jihar Kaduna guda goma sun samu yanci daga hannun tsagerun yan bindigan da suka sacesu ranar 5 ga Yuli, 2021.
TVC ta ruwaito cewa an sako wadannan dalibai ne ranar Asabar, 18 ga Satumba kuma za'a mikasu ga iyayensu.
Har yanzu dai gwamnatin jihar Kaduna da hukumar yan sanda basu tabbatar da labarin ba.
Amma shugaban kungiyar CAN na jihar Kaduna , Joseph Hayab, ya tabbatarwa TheCable labarin cewa an sako ranar Asabar.
Asali: Legit.ng