Da duminsa: Yan bindiga sun sako karin dalibai 10 cikin yan makarantar Bethel Baptist a Kaduna
- Bayan kimanin watanni biyu, an sake sako dalibai 10 cikin wadanda aka sace a Bethel
- Har yanzu yan bindigan basu gama sako daliban da suka sace a makarantar Bethel ba
Kaduna - Akalla karin daliban makarantar Bethel Baptist College dake jihar Kaduna guda goma sun samu yanci daga hannun tsagerun yan bindigan da suka sacesu ranar 5 ga Yuli, 2021.
TVC ta ruwaito cewa an sako wadannan dalibai ne ranar Asabar, 18 ga Satumba kuma za'a mikasu ga iyayensu.
Har yanzu dai gwamnatin jihar Kaduna da hukumar yan sanda basu tabbatar da labarin ba.
Amma shugaban kungiyar CAN na jihar Kaduna , Joseph Hayab, ya tabbatarwa TheCable labarin cewa an sako ranar Asabar.
Legit ta tuntubi Kakakin hukumar yan sandan jihar Kaduna, ASP Muhammad Jalinge, wanda ya bayyana cewa bai tabbatar ba amma zai kiramu idan ya tabbatar.
A cewarsa:
"Barin inyi tambaya, zan kira ka"
Kimanin wata biyu kenan da yan bindiga suka sace dalibai a Bethel Baptist dake Chikun
Tun bayan sace daliban da yan bindiga sukayi ranar 5 ga Yuli, yan bindigan na sakin daliban daki-daki bisa kudin fansan da aka biyasu.
Bayan ana zargin sun karbi miliyan N100m tare da alkawarin sakin daliban Bethel Baptist dake hannunsu kashi-kashi, ɓarayin sun saɓa alkawarinsu.
Yan bindigan sun karya alkawarin da suka yi ne ta hanyar turo da sabuwar bukata ta naira miliyan N50m kafin su sako ragowar ɗalibai 83.
El-Rufai Ya Bada Umurnin Rufe Makarantu 13 a Kaduna
Gwamnatin jihar Kaduna ta bada umurnin rufe wasu makarantu 13 nan take a wurare daban-daban a jihar.
Shugaban sashin kula da ingancin kayayyaki na ma'aikatar ilimi na jihar Kaduna, Umma Ahmed ce ta fitar da sanarwa.
An aike da sanarwar da shugabannin makarantu masu zaman kansu da abin ya shafa, sakon na mai cewa nan take za su rufe makarantun.
Asali: Legit.ng