Neja: 'Yan bindiga sun banka wa sansanin sojojin Najeriya wuta, sun sace motocci da makamai

Neja: 'Yan bindiga sun banka wa sansanin sojojin Najeriya wuta, sun sace motocci da makamai

  • Bayanai sun nuna yadda ‘yan bindiga suka banka wuta a makarantar sakandaren gwamnati ta Allawa a karamar hukumar Shiroro cikin tsakiyar daren Alhamis
  • Har yanzu dai ba samu bayanai dangane da ainihin wadanda lamarin ya shafa ba kasancewar yadda jami’an tsaro suka mayar da makarantar sansanin su
  • Wani jigon matasan Shiroro, Sani Abubakar Yusuf Kokki ya sanar da manema labarai yadda ‘yan ta’addan suka afka sansanin sojin daga bisani kuma suka kai wa jami’an tsaron hadin guiwa farmaki

Jihar Niger - ‘Yan bindiga sun afka makarantar sakandaren gwamnati da ke Allawa a karamar hukumar Shiroro inda suka banka wuta da tsakiyar daren Alhamis, The Nation ta ruwaito.

Duk da dai ba a gano asalin yawan wadanda lamarin ya shafa ba har lokacin rubuta wannan rahoton amma an tattaro bayanai akan yadda suka kai farmakin makarantar wacce ta kasance sansanin jami’an tsaro.

Kara karanta wannan

Fusatattun jama'a sun kai wa tawagar dan majalisar su na tarayya farmaki a Jigawa

Neja: 'Yan bindiga sun banka wa sansanin sojojin Najeriya wuta, sun sace ababen hawa da makamai
'Yan bindiga sun banka wa sansanin sojoji wuta a Neja, sun sace makamai da motocci. Hoto: The Nation
Asali: Twitter

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Sani Abubakar Yusuf Kokki, jigon matasan Shiroro ya sanar da wakilin Daily Trust cewa sun kai farmakin ne kai tsaye sansanin sojin daga baya kuma suka yi wa jami’an tsaron hadin guiwa kwanton bauna.

Ya ce sai da suka sace makamai, motocin suntirin sojoji har da kayan abinci

Kamar yadda ya shaida:

“Yayin kazamin harin, ‘yan ta’addan sun banka wa makarantar sakandaren Allawa wuta wacce yanzu haka sansanin sojoji ce sannan sun sace duk wasu makamai, motocin sintiri, kayan abinci da sauran ababe masu amfani.
“Har yanzu ba a san mutane nawa ne suka tsira ba don wadanda suka tsira suna asibiti rai a hannun Allah. Muna cikin mawuyacin hali don yanzu rayuwa muke yi a karkashin ‘yan ta’adda, sai yadda suka so suke yi da mu. Wannan abin tsoro da takaici ne.”

Kara karanta wannan

Tashin Hankali: Ɗan Sanda Ya Bindige Soja a Fadar Shehun Borno

Ba wannan bane karon farko da suka kai hari yankin ba

Garuruwa da dama sun fuskanci makamancin wannan farmakin daga hannun ‘yan ta’addan wanda ya janyo mace-macen jama’a da dama yayin da wasu suka rasa gidajensu

Duk kokarin da wakilin Daily Trust ya yi wurin tattaunawa da kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, DSP Wasiu Abiodun ya ci tura, don ba a samu lambarsa ba har lokacin rubuta wannan rahoton.

Har ila yau bai mayar da amsar sakon da aka tura masa ba.

'Yan bindiga sun sace mutane 29 a wani ƙauyen Katsina, 'Yan Sanda

A wani rahoton, kun ji cewa mutane 29 ne yan bindiga suka sace yayin harin da suka kai kauyen Godiya a cewar rundunar yan sandan Jihar Katsina.

Mai magana da yawun rundunar a jihar, Gambo Isah, ya tabbatar da adadin mutanen yayin zantawa da Channels Television a ranar Talata.

Kara karanta wannan

Obasanjo: Sai an binciko kuma an hukunta wadanda suka banka wa gona ta wuta

Wasu gungun yan bindiga ne suka kai hari a Ruwan-Godiya a daren ranar Lahadi a karamar hukumar Faskari.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164