An yi fansar Bakano daga hannun 'yan ta'adda da kiret 6 na giya, babura 2 da N500,000

An yi fansar Bakano daga hannun 'yan ta'adda da kiret 6 na giya, babura 2 da N500,000

  • Iyalan wani Bakano wanda 'yan ta'adda suka sace a kan babbar hanyar Kaduna zuwa Abuja sun cika wasu sharuddan fansa masu bada mamaki
  • 'Yan ta'adda sun bukaci kiret 6 na giya, babura 2, kwali 1 na maganin karin karfi da kudi har N500,000 domin fansar Mukhtar Ibrahim
  • Sun ja kunnen 'yan uwan Ibrahim cewa kada su kuskura su saka na'urar gano inda suke a cikin giyar kuma kada su saka guba a ciki

'Yan ta'adda sun sako wani dan asalin jihar Kano mai suna Muktari Ibrahim bayan iyalansa sun cika wasu sharudda masu bayar da mamaki.

Ibrahim wanda aka sace a ranar 21 ga watan Nuwamban 2021 tare da wasu matafiya a kan babbar hanyar Abuja zuwa Kaduna, ya shiga tashin hankali.

An sako shi a ranar Larabar da ta gabata bayan kwashe kusan watanni uku a wurin 'yan ta'addan kamar yadda Daily Nigerian ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Innalillahi: An tsinci gawar mai gadi da iyalansa uku a wani gidan gona a Abuja

An yi fansar Bakano daga hannun 'yan ta'adda da kiret 6 na giya, babura 2 da N500,000
An yi fansar Bakano daga hannun 'yan ta'adda da kiret 6 na giya, babura 2 da N500,000. Hoto daga dailynigerian.com
Asali: UGC

Daily Nigerian ta tattaro cewa tun bayan sace shi, iyalansa sun dinga ciniki da miyagun domin fatan a sako shi. An fara daga miliyan hamsin har suka kai dubu dari biyar, kiret shida na giya, kwali daya na maganin karfi da kuma babura 2 kirar Bajaj.

Majiyoyi daga iyalansa sun ce da farko 'yan ta'addan sun jaddada cewa a kawo musu mashin kirar Boxer guda 2 ba Bajaj ba, amma lokacin da iyalansa suka janyo hankalinsu kan haramta siyar da irin babur din a jihar, sai suka amince da hakan.

Majiyar ta ce:

"Daga bisani sun amince za su karba babur kirar Bajaj tare da kiret shida na giya, kwali daya na maganin karin karfi da kudi dubu dari biyar.
"A yayin cinikin, sun ja kunnenmu kan kada mu saka na'urar gano inda suke ko kuma mu saka guba a giyar. Ko siyan giyar, sai da muka wahala

Kara karanta wannan

Wadanda suka sace yan uwan malamin jami’ar Zamfara sun nemi a biya miliyan N70

“A yayin da aka kai musu kayayyakin bayan sa'o'i kadan da wannan tafiyar wahalan a cikin daji, sun ce za su sako dan uwan mu ne idan sun tabbatar da cewa ba a saka na'urar gane inda suke ba kuma sun gane babu guba a kayan shan.
“Daga nan sai suka sako shi washegarin da aka kai musu kayan. Ba su ba shi kudin mota ba amma sun ce ya roki wani shugaban yanki da ya kai shi hanya.
“Shugaban yankin ya jajanta masa halin da ya shiga kuma ya bashi naira dari uku, wanda yayi amfani da shi ya hau babur zuwa Zaria," daya daga cikin iyalansa wanda ya bukaci a boye sunansa ya sanar.

Kaduna: 'Yan ta'adda sun bindige tsohon dan takarar ciyaman da abokinsa

A wani labari na daban, 'yan bindiga sun harbe tsohon dan takarar shugaban karamar hukuma a zaben kananan hukumomi a jihar Kaduna, Steven Inuwa, a ranar Lahadi da ta gabata a Abuja.

Kara karanta wannan

Nasara: 'Yan sanda sun halaka 'yan ta'adda 23, sun yi ram da 'yan bindiga 37 a Sokoto

Inuwa wanda ya yi takara karkashin jam'iyyar Peoples’ Democratic Party (PDP) ya rasu a asibitin Bwari, Daily Trust ta ruwaito.

Miyagun 'yan ta'addan sun hada da Ernest Agatha sun kashe shi bayan sun harba bindiga kan motarsa da ya ke tukawa wurin yankin Zuma a gefen birnin Bwari, Daily Trust ta ruwaito.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Khalid avatar

Aisha Khalid (Hausa editor) Aisha Khalid marubuciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018. Ta kwashe shekaru tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu. Za a iya tuntubar ta a adireshin email din ta kamar haka: aisha.khaleed@corp.legit.ng