Babu wani amfani: Masari ya nemi a bude iyakokin Katsina yadda aka bude na sauran Jihohi

Babu wani amfani: Masari ya nemi a bude iyakokin Katsina yadda aka bude na sauran Jihohi

  • Rt. Hon. Aminu Bello Masari ya halarci wani taro da shugaban kwastam na shiyyar Katsina ya shirya
  • Gwamna Masari ya yi kira ga hukumar NCS ta yi la’akari da bude iyakokin da su ke jihar Katsina
  • Sakataren gwamnati, Dr. Mustapha Inuwa shi ne ya wakilci Mai girma Gwamnan jihar Katsina a taron

Katsina – Mai girma Gwamnan jihar Katsina, Aminu Bello Masari ya yi kira ga hukumar kwastam ta duba toshe rufe iyakokin kasarta da aka yi.

Daily Trust ta kawo rahoto a yammacin Alhamis, 3 ga watan Fubrairu 2022 cewa Aminu Bello Masari ya yi wannan kira ne a wajen wani taro da aka yi.

Sakataren gwamnatin Katsina, Dr Mustapha Inuwa ya wakilci gwamnan a wajen wannan zama da shugaban kwastam na shiyyar ta Katsina ya kira a jiya.

Kara karanta wannan

Gyadar doguwa: Gwamna ya canza rayuwar 'yan mata 2 daga haduwa da su a hanyar kauye

Gwamnan ya fadawa DC Dalha Wada Chedi cewa rufe iyakokin da aka yi na tsawon lokaci bai kawo abin da ake nema ba, don haka ya kamata a bude su.

Rt. Hon. Aminu Bello Masari ta bakin Dr. Mustapha Inuwa ya ce rufe iyakokin ba zai yi wani tasiri ba har sai an fadakar da al’umma kan abin da ya kamata.

Kwastam
Jami'an kwastam a bakin aiki Hoto: AFP
Asali: UGC

Jawabin da Gwamna ya yi

“Tunaninmu shi ne jami’an kwastam za su fito da wani gamsasshen tsari a kan yadda mutane za su cigaba da neman halaliyarsu cikin sauki.”
“Ta yadda da zarar an dawo an bude iyakoki, mutane ba za su koma su cigaba da aikin masha’a da suka saba yi a baya ba.” – Aminu Masari.

Jaridar ta rahoto Gwamnan na Katsina yana cewa garkame iyakokin bai yi maganin fasa kauri ba.

Kara karanta wannan

Rikicin Kano: Mala Buni ya yi zama da Shekarau da manyan APC da ke fada da Ganduje

“Rufe iyakokin bai canza fasa-kaurin da ake yi ba saboda mutanen da suka saba neman abinci ta wannan hanyar, dole su nemi abin da za su sa a bakunansu.”
“Abin da yake faruwa a Maigatari, shi ne yake faruwa a Kamba, Illela da Jibiya da sauran iyakoki, abin da ya dace shi ne neman hanyar samun kudin-shiga."

- Aminu Masari

A karshe sakataren gwamnatin ya godewa shugaban kwastam a kan kokarin da ya yi wajen gyara alakar da ke tsakanin jami’ansa da sauran al’ummar jihar Katsina.

Sanwo Olu ya ceci 'yan mata

A ranar Alhamsi ne aka ji labari cewa Gwamnan jihar Legas, Babajide Sanwo Olu ya yi kicibis da wasu mata da suke yawo a lokacin da sa’o’insu su ke aji a makaranta.

Amarachi Chinedu da Suwebat Husseini za su je kai wa iyayensu markade ne sai gwamnan ya hange su, yanzu maganar da ake yi za a dauki dawainiyar karatunsu.

Kara karanta wannan

Na sanar da Atiku cewa ya tsufa kuma gajiye ya ke, ba zai iya shugabanci ba, Gwamnan Bauchi

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng