An kashe jami’an yan sanda uku, an sace mazauna da dama yayin da yan bindiga suka kai hari a Neja
- Yan bindiga sun kashe a kalla jami'an yan sanda uku a wani farmaki da suka kai ofishinsu a garin Ishau da ke karamar hukumar Paikoro ta jihar Neja
- Mummunan al'amarin ya afku ne lokacin da maharan suka isa ofishin don sakin wani mai yi masu kwarmato da aka tsare
- Sun kuma farmaki garuruwa 11 da suka hada da Zubakpere, Kuna, Aboloso, Kudami, Dakolon Daji, Nugwazi, Amale, Adunu, Ishau da wani bangare na Beni
Niger - Yan bindiga sun kashe jami’an yan sanda uku a wani samame da suka kai ofishin yan sanda da ke Ishau karkashin Kafin-koro a karamar hukumar Paikoro ta jihar Neja.
An tattaro cewa yan bindigar sun kai mamaya ofishin yan sandan su da yawa don sakin wani mai masu kwarmato wanda ke tsare, jaridar The Nation ta rahoto.
Sun kashe jami’ai uku yayin da sauran suka gudu a lokacin harin.
Nigerian Tribune ta kuma rahoto cewa bayan harin, yan bindigar sun kuma gudanar da farmakin kauye bayan kauye a yankin Kafin Koro.
garuruwa 11 da suka hada da Zubakpere, Kuna, Aboloso, Kudami, Dakolon Daji, Nugwazi, Amale, Adunu, Ishau da wani bangare na Beni.
An yi garkuwa da wasu da dama ciki harda hakimi, yaransa hudu da mata biyar a fadin garuruwa shida da ke karamar hukumar.
Ba a samu jin ta bakin kakakin yan sandan jihar Neja, DSP Wasiu Abiodun ba, don bai dauki waya ba.
Ka tabbatar ka tsare Kaduna kafin ka yi ritaya, Shehu Sani ga Buhari
A wani labarin, tsohon sanata da ya wakilci Kaduna ta tsakiya a majalisar dattawa, Shehu Sani, ya ba shugaban kasa Muhammadu Buhari, shawara a kan tsare-tsaren ritayar shi.
Sani ya bayyana cewa akwai bukatar gwamnati mai ci ta kawar da ta’addanci da kawo karshen duk wasu nau’i na ta’addanci kafin shugaban kasar ya ji dadin ritayansa.
A ranar 18 ga watan Disamba ne Buhari yace yana Allah Allah 2023 yayi don ya mika mulki ga sabon shugaban kasa sannan ya koma ga gonarsa.
Asali: Legit.ng