Abin kunya ne ga Najeriya: Sanatan APC ya koka kan yawaitar garkuwa da mutane a ƙasar

Abin kunya ne ga Najeriya: Sanatan APC ya koka kan yawaitar garkuwa da mutane a ƙasar

  • Adamu Aliero, sanata mai wakiltar Kebbi ta tsakiya ya kwatanta karuwar garkuwa da jama’a da ke aukuwa a kasar nan da tozarcin a idon duniya
  • Ya yi wannan furucin ne yayin wani taron muhawara wanda Bello Mandiya, Sanata mai wakiltar Katsina ta kudu ya shirya
  • Mandiya ya janyo hankalin ‘yan uwan aikin sa akan garkuwa da fiye da mutane 30 da aka yi a karamar hukumar Batsari, cikin Jihar Katsina

Jihar Katsina - Adamu Aliero, sanata mai wakiltar Kebbi ta tsakiya ya kwatanta garkuwa da mutanen da ke ta karuwa a kasa a matsayin abin kunya ga Najeriya, The Cable ta ruwaito.

Aliero ya yi wannan maganar ne ranar Laraba yayin wani taron muhawara da Bello Mandiya, Sanata mai wakiltar Katsina ta Kudu ya shirya.

Kara karanta wannan

Kisan gilla: Bayan kisan Hanifa, wani Malami ya kashe Almajirinsa a jihar Kano

Abin kunya ne ga Najeriya: Sanatan APC ya koka kan yawaitar garkuwa da mutane a kasar
Sanatan APC ya koka kan yawaitar garkuwa da mutane a kasar, ya ce abin kunya ne. Hoto: The Cable
Asali: Twitter

Mandiya ya janyo hakalin takwarorinsa a kan garkuwa da fiye da mutane 30 da ‘yan bindiga suka yi a karamar hukumar Faskari da ke Jihar Katsina.

Ya ce ya kamata a dauki matakan gaggawa

Yayin tsokacin, The Cable ta nuna yadda sanatan na Jihar Kebbi ya ce ya kamata a dauki matakai cikin gaggawa don kawo karshen garkuwa da mutane a kasar nan.

Kamar yadda ya furta:

“Abin kunya ne ga kasar nan ace ana ci gaba da irin wannan mummunan aiki a ko wacce rana. Ya kamata a bai wa jami’an tsaro hadin kai.”

Ya ce a dauki sabbin ‘yan sanda idan bukatar hakan ta tashi

Ya kara da cewa idan akwai bukatar a kara daukan ‘yan sanda ne, ya kamata a yi hakan.

Kara karanta wannan

Mafita kawai duk yan bindigan da aka kama a tura su ga Allah, Sarki ya ɗau zafi

A cewarsa:

“Batun rashin yawan ‘yan sanda a kasar nan abin dubawa ne. Muna bukatar ‘yan sanda sosai. Idan akwai bukatar a kara daukar wasu aiki, mai ze hana ayi hakan?”

'Yan bindiga sun sace mutane 29 a wani ƙauyen Katsina, 'Yan Sanda

A wani rahoton, kun ji cewa mutane 29 ne yan bindiga suka sace yayin harin da suka kai kauyen Godiya a cewar rundunar yan sandan Jihar Katsina.

Mai magana da yawun rundunar a jihar, Gambo Isah, ya tabbatar da adadin mutanen yayin zantawa da Channels Television a ranar Talata.

Wasu gungun yan bindiga ne suka kai hari a Ruwan-Godiya a daren ranar Lahadi a karamar hukumar Faskari.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164