'Yan daba sun kutsa wani coci a Legas, sun lakaɗa wa fasto da masu gadi duka

'Yan daba sun kutsa wani coci a Legas, sun lakaɗa wa fasto da masu gadi duka

  • Wasu ‘yan bindiga sun afka harabar cocin Holy Trinity da ke lamba 2 a Oba Adeyemi Oyekan Avenue a garin Ikoyi da ke Jihar Legas
  • Faston da ke kula da cocin, John Delano da masu gadin cocin guda biyu sun sha da kyar sakamakon farmakin da ‘yan daban suka kai
  • Sun afka cikin cocin ne da buldoza inda suka rusa katangar da ke gaba tare da tumbuke bishiyoyi da kofofin cocin

Jihar Legas - Wasu ‘yan daba sun kai farmaki cocin Holy Trinity da ke lamba 2 a Oba Adeyemi Oyekan Avenue a cikin garin Ikoyi da ke Jihar Legas, Vanguard ta ruwaito.

Faston da ke kula da cocin, John Delano, wani ma’aikacin cocin da masu gadi biyu sun tsira da kyar sakamakon harin da suka kai.

Kara karanta wannan

Nasara: 'Yan sanda sun halaka 'yan ta'adda 23, sun yi ram da 'yan bindiga 37 a Sokoto

'Yan daba sun kutsa coci sun yi wa fasto da mai gadi duka a Legas
Yan daba sun afka cikin wani coci a Legas, sun yi wa fasto da mai gadi duka. Hoto: Vanguard
Asali: Twitter

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Fiye da ‘yan daba 30 ne suka afka cocin da buldozar bayan kammala taron addu’o’i na safe inda suka rushe katangar gaban cocin tare da tumbuke kofofi da wasu bishiyoyi manya guda uku.

Babban faston cocin ya sha mari a hannun ‘yan daban

Yayin kai farmakin, Fasto John Delano David da wasu masu gadi biyu sun sha mari da duka, inda aka kusa halaka masu gadin da aka tanada musamman don kulawa da wurin.

A cewar Delano:

“A ranar Laraba da safe, ni da David Neji (mai kula da cocin) muna shirin rufe cocin bayan kammala addu’o’in safe da aka yi daga karfe 6 na safe zuwa karfe 7 muka ji hayaniya. Muna leka wa muka ga buldoza tana cire mana kofar da kuma wasu maza sun kai 30 suna shiga cocin.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: 'Yan bindiga sun kai sabon hari, sun sace mutane kusan 60 a Katsina

“Mutumin da ke gaba ne yake ta basu umarni. Yana cewa kowa ya fita. Bayan jin umarnin nashi ne mu ma muka fara biyayya. Bayan na tuna na bar makullin mota ta a coci ne nayi saurin komawa don in matsar da motar gefe guda.
“Lokacin da na zo na tarar ana dukan masu gadin mu biyu sai na ciro waya ta na hau daukar hotuna da bidiyo. Ina tsaka da dauka ne cikin ‘yan daban wani ya kwace waya ta ni kuma na hau bin shi. Anan ya kai ni wurin shugaban su mai sanye da koriyar riga.”

Kudin hayar cocin bai kare ba sai watan Nuwamba

Bayan nan ne yace shugaban nasu ya mare shi. Daga nan kowa ya hau marin shi wanda har sai da suka kai shi kasa.

Delano ya bayyana yadda suka tambaye shi ko wanene shi inda yace musu shi fasto ne. Kuma sun biya kudin hayar cocin wanda sai watan Nuwamban 2022 zata kare.

Kara karanta wannan

Basarake da 'yan tawagarsa na asibiti rai a hannun Allah bayan harin da aka kai masa

A cewarsa, tun kafin nan sun dinga bukatar a siyar musu da wurin amma an ki. Yayin da aka kasa daidaita wa ne suka ce zasu kore su.

Sun bukaci su biya su ragowar kudin hayar cocin, su kuma suka ki yarda daga nan ne suka fara tayar musu da hankali har sun kai su kara babbar kotun Jihar Legas.

Vanguard ta gano yadda tun bayan harin ‘yan sanda ba su mayar da hankali akan daukar mataki ba. Wani babban dan sanda ya ce bai san abinda zai yi ba don kwace fili a Ikoyi ya zama ruwan dare.

'Yan sanda sun yi ram da wasu samari 2 bayan sun datse wa juna hannaye yayin kwasar dambe

A wani labarin, 'yan sanda sun yi ram da samari 2 bisa kama su dumu-dumu da laifin sare wa juna hannaye, kamar yadda jaridar Premium Times ta ruwaito.

An ruwaito yadda ‘yan sandan su ka kama Adamu Mohammed da Bukar Audu, bayan sun datse wa juna hannaye yayin wani fada da su ka tafka a Garin Alkali, karamar hukumar Dapchi da ke jihar Yobe.

Kara karanta wannan

Niger: Rayuka birjik sun salwanta, gidaje sun babbake a sabon harin ƴan ta'adda

Premium Times ta bayyana yadda Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, Dungus Abdulkarim, a ranar Litinin a Damaturu ya bayyana a wata takarda.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164