Gwanda na mutu, mutumin da aka ce sai an yiwa rigakafin Korona kafin ayi masa dashin koda yace

Gwanda na mutu, mutumin da aka ce sai an yiwa rigakafin Korona kafin ayi masa dashin koda yace

  • Wani dan kasar Amurka Chad Carswell yace ba zai yarda ayi masa rigakafin Korona ba, sai dai ya mutu
  • Likitocin asibiti kuwa sun ce ba zasu yi masa dashin koda ba sai an yi masa rigakafin cutar Korona
  • Saura kiris kodarsa ta gama lalacewa kuma idan ba'ayi masa dashin ba yana iya mutuwa

Amurka - Wani mutumi ya yi watsi da dashin kodar da ake shirin masa saboda jami'an asibitin sunce wajibi ne a yi masa rigakafin cutar Korona kafin ayi masa dashin.

Mutumin mai suna Chad Carswell dan garin North Carolina a kasar Amurka yace gwanda ya mutu da ayi masa rigakafin.

Carswell ya bayyanawa WSOC-TV cewa:

"Kyauta aka haifeni. Kyauta zan mutu. Ban zan canza ra'ayi na ba. Na tattauna da iyalina da dukkan makusantana. Sun san matsayata kuma babu abinda zai sa in canza ra'ayi na kan wannan lamari."

Kara karanta wannan

Bana so na daurawa kowa nauyi: Dattijo ya gina kabarinsa, ya siya duk abun da za a sha a yayin bikin mutuwarsa

Korona kafin ayi masa dashin koda yace
Gwanda na mutu, mutumin da aka ce sai an yiwa rigakafin Korona kafin ayi masa dashin koda yace Hoto: (WSOC)
Asali: Facebook

Kodar Carswell yanzu haka ta kusa lalacewa kuma yana bukatar wankin koda sau uku kowani mako.

Yan uwa da abokan arzikinsa sun tara masa kudi kuma sama da mutum dari sun yi alkawarin bashi kyautar koda.

Amma jami'in asibitin Atrium Health Wake Forest Baptist a Winston-Salem ya bayyana cewa wajibi a yi masa rigakafin tare da wanda ke shirin bada koda.

Yace:

"Na fada masa kada ya bata lokacinsa wajen maganar rigakafin nan. Sai ya fada min, 'Amma ka san zaka mutu idan baka yi ba ' Sai na ce masa, 'Shirye nake na mutu."

Mr Carswell yace yanzu suna kan neman wani asibitin daban don yi masa dashin kodar.

Likitoci sun samu nasarar dasawa dan Adam kodar Alade a Amurka

Kara karanta wannan

Dillalin gidaje ya mutu a dakin Otal bayan shakatawa da matar aure

A baya mun kawo muku cewa an samu nasarar dasa kodar Alade cikin dan Adam ba tare da wata matsala ba, wani sabon bincike da ka taimakawa mutane masu matsalar cutar koda.

Reuters ta ruwaito cewa an gudanar da wannan aiki ne a jami'ar New York dake kasar Amurka.

An yi amfani da kwayar hallitar Aladen da aka canza ne bayan cire wani kwaya wanda zai iya kawo matsala jikin mutum, binciken ya nuna.

An gwada wannan bincike ne kan mara lafiyar da kwakwalwarta ta mutu kuma take fama da ciwon koda bayan amincewar iyalansa, masu binciken suka bayyanawa Reuters.

Tsawon kwanaki uku, an dasa sabon kodar cikin jininta amma ba'a dinke ba domin ganin yadda abun zai gudana.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdul Rahman Rashid avatar

Abdul Rahman Rashid Rashidah Abdul Rahman 'yar jarida ce kuma dalibar ilimi wacce ta kwashe shekaru kimanin hudu yanzu tare da shararriyar jarida Legit. Ta samu gogewa a ɓangaren rubutun labarai akan fannoni shatta, wanda suka hada da siyasa, kasuwanci, wasanni, nishadi, dss. Zaku tuntubarta a akwatin email: abdulrahman.rashidah@corp.legit.ng

Online view pixel