Da dumi-dumi: Yan bindiga sun bindige yayan kwamishina a jihar Benue
- Tsagerun yan bindigan da ba a san ko su wanene ba sun bindige Christopher Inalegwu, yayan kwamishinan labarai, al’adu da yawon bude ido na jihar Benue
- Maharan sun harbe Inalegwu ne a gonarsa da ke kauyen Aku, gudunmar Okololo da ke karamar hukumar Agatu ta jihar
- Marigayin mai shekaru 65 ya kasance dan uwa guda daya tilo da kwamishinan ke da shi
Benue - Yan bindiga sun harbe Christopher Inalegwu, yayan kwamishinan labarai, al’adu da yawon bude ido na jihar Benue, jaridar Daily Trust ta rahoto.
An harbe Inalegwu ne a gonarsa da ke kauyen Aku, gudunmar Okololo da ke karamar hukumar Agatu, a ranar Litinin, 31 ga watan Janairu.
Shaidu sunce marigayin mai shekaru 65 na aiki a gonarsa ne lokacin da yan bindigar suka far masa sannan suka bude masa wuta.
Nigerian Tribune ta rahoto cewa kamishinan labaran, Michael Inalegwu, ya ce harin ba na tunzurawa bane.
Ya koka a kan rashin dan uwa daya tilo da ya rage masa, inda ya ce duk da radadin da suke ciki, mutanen Agatu da Benue ba za su mika wuya ga miyagun mutane ba.
Inalegwu ya ce bayan an harbi dan uwan nasa, an dauki dan lokaci kafin a taimaka masa zuwa wani asibiti da ke kusa amma babu likita a wurin.
Ya kara da cewa daga bisani an dauki dan uwansa da ya samu munanan raunuka zuwa wani asibiti inda ya mutu ‘yan mintoci da isar su.
Ya ce:
“Sun bude masa wuta a gonarsa da ke Aku a Agatu. Ba za a tursasa mu mika kasarmu ba.”
Kwamishinan ya bayar da tabbacin cewa gwamnatin jihar za ta yi duk mai yiwuwa wajen ganin an samar da tsaro a yankunan Gwer West da Agatu na jihar inda a halin yanzu ake kai wa mazauna yankin hari.
Da aka tuntube shi, kakakin ‘yan sandan Benue, SP Catherine Anene, ta ce har yanzu ba ta samu rahoton faruwar lamarin ba.
A wani labarin na daban, mun ji cewa, an kama wani likita da ake zargin ya yi jinyar harbin bindiga ga dan ta'adda Bello Turji a jihar Sokoto.
An kama likitan mai suna Abubakar Kamarawa ne a wani gagarumin samame da jami’an tsaro suka kai kan 'yan ta'addan.
An kama shi ne tare da wasu 'yan ta'addan a wasu ayyuka daban-daban a fadin kananan hukumomi uku na jihar Sokoto.
Asali: Legit.ng