Aikin 'yan sanda: An fitar da sanarwa mai muhimmanci tare da ranakun tantancewa

Aikin 'yan sanda: An fitar da sanarwa mai muhimmanci tare da ranakun tantancewa

  • 'Yan sanda sun fitar da wani muhimmin bayani game da masu sha'awar shiga aikin da suka cike foma-foman nuna sha'awar aiki
  • A cewar kakakin rundunar, CP Frank Mba, wadanda suka fito daga yankin Arewacin kasar nan sun fi na wadanda suka fito daga yankin kudu yawa
  • Shugaban ‘yan sanda, Usman Baba ya umurci mutanensa da su tabbatar da cewa ‘yan asalin jihohi ne kawai za a tantance a tantancewar da za a fara a ranar 1 ga Fabrairu ta kare ranar 20

A wani labari da zai faranta ran 'yan Najeriya, rundunar 'yan sandan Najeriya ta sanar da fara tantance daukar ma'aikata ta 2021 da ke gudana.

Akalla mutane 127,491 ne suka cike fom din shiga aikin ‘yan sanda da aka sa ran za su hallara a ranar Talata 1 ga watan Fabrairu a hedikwatar ‘yan sanda ta jihohi a fadin kasar domin a duba lafiyarsu.

Kara karanta wannan

Gwamnatin Buhari ta amince a bada kwangilolin wasu tituna 16 da za su ci Naira Biliyan 64

Batun daukar 'yan sanda aiki
Aikin dan sanda: 'Yan Arewa 104,403, 23,088 'yan kudu ne suka nemi aiki a 2023 | Hoto: vanguardngr.com
Asali: UGC

Jaridar The Punch ta ruwaito cewa wadanda suka nemi shiga aikin sun kunshi mutum 104,403 daga yankin Arewa sai kuma mutane 23,088 daga Kudancin kasar nan.

Dalla-dalla: Jihohi da adadin mutanen da suka nuna sha'awarsu ga aikin dan sanda

1. Jihohin Kudu

  1. Abia state has 596
  2. Akwa Ibom 3,536
  3. Anambra 314
  4. Bayelsa 759
  5. Cross River 2,704
  6. Delta 976
  7. Ebonyi 463
  8. Edo 1,206
  9. Ekiti 1,417
  10. Enugu 707
  11. Imo 852
  12. Lagos 562
  13. Ogun 1,154
  14. Ondo 2,472
  15. Osun 2,006
  16. Oyo 1,767
  17. Rivers 1,597

2. Jihohin Arewa

  1. Plateau 4,100
  2. Kebbi 3,596
  3. Katsina 7,605
  4. Kano 7,557
  5. Kaduna 7,436
  6. Jigawa 4,951
  7. Benue 6,578
  8. Adamawa 8,206
  9. Bauchi 7,140
  10. Borno 8,693
  11. Federal Capital Territory 4,418
  12. Kogi 4,412
  13. Kwara 2,410
  14. Nasarawa 4,700
  15. Niger 4,672
  16. Sokoto 2,450
  17. Taraba 4,075
  18. Yobe 4,992
  19. Gombe, 4,416
  20. Zamfara 1,990

Kara karanta wannan

Kotu ta zabi ranar Valentine don yanke wa Hushpuppi hukunci a Amurka

Ranar da za a fara tantancewa

Sakon da aka fitar daga hukumar ya umurci masu neman shiga aikin su hallara a hedkwatocin 'yan sanda a jihohin kasar nan daga ranar 1-20 ga Fabrairu.

Jerin abubuwan da masu nema za su zo tare da su

Rundunar a shafinta na Facebook ta umurci masu neman shiga aiki da su zo da lambar shaidar kasa ta NIN, na asali da kwafin takardunsu, takaddun shaidar asali, takaddun haihuwa ko bayyana shekaru, takardar shaidar sun cike fom da kuma cikakkun takaddun shaidu.

Ta kuma yi gargadi game da a gujewa cin hanci da rashawa tare da gargadin jami’ai su bi ka’idojin da aka gindaya a dokar hukumar ‘yan sanda.

A wani labarin, hukumar aikin yan sanda (PSC) ta umurci Sifeto Janar na yan sanda, Usman Baba Alkali, ya kaddamar da sabon bincike kan alakar dake tsakanin dakataccen jami'i Abba Kyari, da dan damfara, Abbas Ramon, wanda aka fi sani da Hushpuppi.

Kara karanta wannan

Da Dumi-Dumi: Yan bindiga sun yi awon gaba da ɗan uwan tsohon shugaban ƙasa a Najeriya

A cewar Sahara Reporters, wannan umurni ya biyo bayan shawarar da Antoni Janar na kasa kuma Ministan Shari'a, Abubakar Malami, ya bada.

Rahoton yace a ranar Laraba, 26 ga Junairu, Antoni Janar yace hujjojin dake cikin takardan binciken da aka gudanar basu da karfin da za'a kama Abba Kyari da laifi a kotu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.