Labari da ɗuminsa: Boko Haram sun sako ƴan mata 4 na Chibok da suka sace
- 'Yan ta'addan Boko Haram sun sako 'yan mata hudu daga cikin wadanda suka sace a garin Chibok yayin farmakin da suka kai
- A makonni biyu da suka gabata, 'yan ta'addan sun kai farmaki inda suka sace mutum tara, sun sako tsofaffin mata biyu da kananan yara
- An gano cewa sun kwashe 'yan matan inda suka lula yankin Dille da ke karamar hukumar Askira Uba, wurin da ke da iyaka da dajin Sambisa
Borno - 'Yan ta'adda da ake zargin mayakan ta'addanci ne na ISWAP wadanda suka kai farmaki kauyen Kautikari da ke karamar hukumar Chibok ta jihar Borno sun sako 'yan mata hudu da suka sace a ranar Juma'a, 14 ga watan Janairun 2022.
Idan za mu tuna, a yayin farmakin, an sace mazauna yankin Kautikari tara kafin daga bisani su sako tsofaffin mata biyu da kananan yara, sai dai sun dauke 'yan mata hudu inda suka tafi da su kauyen Dille da ke kusa da Askira Uba, karamar hukumar da ke da iyaka da Sambisa.
A yayin farmakin, sun kone majami'a tare da gidajen jama'a, ciki har da katafaren gidan wani dan kasuwa suka babbaka, Vanguard ta ruwaito.
Kautakiri ya na gabas kuma akwai nisan kilomita 15 daga garin Chibok wanda da yawa mazauna garin Kiristoci ne.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Sirikin dan kasuwan wanda ya bukaci a boye sunansa kuma ya na zama a Maiduguri, ya tabbatar da sako 'yan matan, Vanguard ta ruwaito.
"Zan iya tabbatar muku da cewa 'yan mata hudu da ke hannun 'yan ta'adda sun samu 'yanci a ranar Lahadi.
"An sanar da ni cewa an kai su yankin Dille ta karamar hukumar Askira Uba a jihar Borno, inda ke da iyaka da dajin Sambisa.
"A halin yanzu dukkan 'yan matan suna hannun hakimin Kautikari wanda ke zama a birnin Chibok," yace.
Nasara: Soji sun bankado farmakin 'yan ta'adda, sun ceto dan siyasa da iyalinsa a Zamfara
A wani labari na daban, sojoji tare da taimakon 'yan sa kai a daren Asabar sun ceto wani dan siyasa da iyalansa bayan musayar wuta da suka yi da 'yan ta'addan inda aka kashe 'yan ta'adda masu yawa.
Majiyoyi daga Gusau, babban birnin jihar Zamfara, sun tabbatar wa da Premium Times cewa, an sace dan siyasa Aminu Adamu a gidan sa da ke kwatas din Mareri da ke birnin.
Adamu wanda aka fi sani da Papa, shi ne manajan daraktan hukumar sufuri ta jihar Zamfara kuma makusancin Gwamna Bello Matawalle.
Wani mazaunin yankin mai suna Zayyanu Muhammad, ya sanar da cewa 'yan ta'addan sun bayyana a babura inda kai tsaye suka tsinkayi kwatas din Mareri inda Adamu da iyalansa su ke.
Asali: Legit.ng