Abba Kyari ya goge duk wallafarsa ta Facebook bayan zuba kusan hotuna 462 na bikin dan IGP
Abba Kyari, mataimakin kwamishinan 'yan sanda a Najeriya, ya goge dukkan wallafar sa ta shafinsa na Facebook jim kadan bayan ya zuba hotunan bikin Maina Alkali, dan Usman Baba, sifeta janar na 'yan sandan Najeriya, wanda ya halarta a Maiduguri.
Jim kadan bayan ya yi wallafar, kafafen yada labarai masu yawa sun dinga bayyana cewa wannan ce fitar sa ta farko cikin jama'a bayan da aka fara bincike kan sa, hakan ya sa ya gobe dukkan wallafar sa.
Bayyanar Kyari a bikin shi ne fitar sa cikin jama'a na farko tun bayan da aka fara bincikar sa kan zargin hannun sa cikin wata gagarumar damfara.
Kamar yadda wata kotun Amurka ta bayyana a shekarar da ta gabata, Hushpuppi, wanda asalin sunan sa Ramon Abbas, an zargi ya bai wa Abba Kyari cin hanci dmin ya kama wani dan damfara mai suna Vincent.
Hushpuppi, dan damfara da ya amsa laifinsa da bakin sa, an damke shi a hadaddiyar daular larabawa kuma ana zarginsa da damfarar mutum 1.9 miliyan kudi da ya kai N168 biliyan.
Dan damfarar ya ce ya bai wa Abba Kyari kudi domin ya kama tare da aike wani abokin hamayyarsa na Najeriya zuwa gidan yari kan rikicin wata damfarar wasu 'yan kasuwar Qatar $1.1 miliyan.
A wannan lokacin, Kyari ya musanta karbar kudin inda ya jaddada cewa hannayensa tas suke.
DCPn daga bisani ya tabbatar ya san zancen kudin amma kuma bayan damke Vincent ya bayar da belinsa.
An dakatar da Kyari matsayin kwamandan IRT a watan Augusutan da ya gabata kuma an kafa kwamitin bincike a kan sa.
Yayin da aka kaddamar da sabon bincike kansa, Abba Kyari ya halarci auren 'dan IGP Alkali
A wani labari na daban, tsohon shugaban rundunar IRT, Abba Kyari, a ranar Asabar ya halarci daurin auren Maina Alkali, dan gidan Sifeto Janar na yan sanda, IGP Usman Alkali Baba.
Wannan ya biyo bayan bude sabon shafin bincike da hukumar aikin yan sanda tayi a akansa.
Bayan watanni shida da hijra daga kafafen ra'ayi da sada zumunta, Abba Kyari ya daura hotunan yadda ya halarci daurin auren.
Asali: Legit.ng