An bada aikin titin da zai sa dole mutanen unguwanni 16 su canza matsuguni a Abuja

An bada aikin titin da zai sa dole mutanen unguwanni 16 su canza matsuguni a Abuja

  • Wani aikin hanya da za a yi a karamar hukumar Bwari zai tilastawa wasu mazauna barin yankin
  • Masu zama a Utako, Maje, Mabushi, Jabi Samuel, Jabi Yakubu, duk za su nemi wani wurin zama
  • Mazauna yankin za su rabe kafin a kammala gina titi daga Mpape zuwa unguwar Shere-Galuwyi

FCT Abuja - Mutane daga wasu unguwanni 16 za su bar gidajensu, su shigo karamar hukumar Bwari a babban birnin tarayya domin a rage cinkoso.

Jaridar The Whistler ta ce mazauna wasu yankuna za su shigo Bwari ne domin gwamnati ta iya kokarin shawo karshen tabarbarewar da birnin yake yi.

Hakan na zuwa ne bayan majalisar zartarwa ta kasa ta amince a kashe Naira biliyan 5.4 wajen gina titi daga Mpape zuwa yankin Shere-Galuwyi a Bwari.

Kara karanta wannan

Gwamnan APC ya yi alkawarin ba Bola Tinubu mutum 1500 da za su taya shi yakin zabe

Kamar yadda mu ka samu rahoto, wannan titi mai tsawon kilomita 14.15 da za a dauko daga unguwar Mpape zai tike a rukunin gidaje da Shere-Galuwyi.

Inda aikin zai taba

Wadanda za a tada a sanadiyyar aikin sun hada da mutanen Utako, Maje, Mabushi, Jabi Samuel, Jabi Yakubu, Kpaadna, Zhilu, Gwarimpa, da kuma Galadima.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Sannan wannan aiki da zai ci fiye da Naira biliyan biyar zai shafi mazauna unguwannin Jahi I, Jahi II, Kado Bimiko, Kado Kuchi, Lungu, Gishiri, da Daki Biu.

Abuja
Ministan birnin Abuja, www.vanguardngr.com

Sakataren yada labarai na Ministan tarayya, Anthony Ogunlelye ya ce Malam Muhammad Bello ya bada sanarwar cewa FEC ta amince da wannan kwangila.

Muhammad Bello ya fitar da jawabi na musamman dauke da wannan sanarwa a ranar Alhamis.

Yadda za a bullowa lamarin

Da farko za a fara dauke mutanen da gidajensu suke a Utako, Maje, Mabushi, Jabi Samuel, Jabi Yakubu, Kpaadna da kuma Zhilu, a nema masu wajen zama.

Kara karanta wannan

Dan majalisa daga Gombe ya lissafo gwanayensa, ya ce daya daga cikinsu ne ya cancanci ya gaji Buhari

Daga baya aikin zai iso ga wadanda suke zaune a sauran unguwannin. Idan ba a yi wannan aikin ba, birnin zai cigaba da tabarbarewa baya ga matsalar tsaro.

Ministan ya ce kamfanin Messrs Vipan Global Investment Resources Ltd aka ba wannan kwangila.

FEC ta yi zama

A ranar Laraba, 26 ga watan Junairu 2022, aka ji cewa majalisar zartarwa ta kasa tayi taron da ta saba duk mako a fadar shugaban kasa da ke birnin Abuja.

Majalisar ta FEC ta amince a kashe N64,686,536,230 a kan wasu ayyukan tituna da za ayi a kasar nan. Daga ciki akwai hanyar Mpape zuwa Shere-Galuwyi.

Asali: Legit.ng

Online view pixel