Shugabannin Musulmi Sun Koka - Najeriya Bata Taɓa Shiga Mawuyacin Hali Irin Yanzu Ba
- Shugabannin Majalisar Koli ta Shari'a a Najeriya (SCSN) sun ce musulmin Najeriya ba su taba shiga muwuyacin hali irin na yanzu ba
- Nafiu Baba Ahmad, Babban Sakataren SCSN ya ce babban abin da ke ciwa musulmin tuwo a kwarya shine kallubalen tsaro, sai kuma wasu abubuwa kamar talauci, tarbarbarewar tarbiyya ds
- Kwamishinan Hukumar Zabe, INEC a Kaduna, Dr Asma'u Sani Maikudi ta bukaci shugabannin musulmi su bukaci mabiyansu da su fita su yi rajistan katin zabe na PVC gabanin 2023
Kaduna - Yan Najeriya musamman musulmi da ke arewa ba su taba tsintan kansu a mawuyacin hali kamar yanzu ba, a cewar shugabannin Majalisar Koli ta Shari'a a Najeriya (SCSN), Vanguard ta ruwaito.
Nafiu Baba Ahmad, Babban Sakataren SCSN ya ce cikin dukkan abubuwan da suka matsawa rayuwar musulmi a yau a Najeriya babu kamar halin rashin tsaro.
Ya yi wannan maganan ne a hedkwatar kungiyar Jama'atul Nasril Islam (JNI) da ke Kaduna kamar yadda Vanguard ta ruwaito.
Baba Ahmad ya lissafa wasu abubuwan da suka tattaru suka kuntatawa rayuwar musulmi inda ya ce akwai talauci, tabarbarewar tarbiyya, ta'amulli da miyagun kwayoyi, cin amana da sauransu.
Kwamishinan INEC a Kaduna ta shawarci mutane su mallaki PVC
A jawabinta, Kwamishinan Hukumar Zabe, INEC a Kaduna, Dr Asma'u Sani Maikudi ta bukaci shugabannin musulmi su bukaci mabiyansu da su fita su yi rajistan katin zabe su kuma samu PVC dinsu gabanin zaben 2023.
Ta jadada muhimmancin samun katin na dindin wato PVC, tana mai cewa an saukaka yadda za a yi rajistan katin zaben ta yadda duk wani mai wayar salula mai intanet zai iya yin rajistan daga gidansa.
Ta kuma ce akwai ofisoshin INEC a kusan dukkan kananan hukumomi na jihar ta kuma bada tabbacin cewa an kara yawan akwatun zabe domin saukaka wa mutane wahalhalu a ranar zaben.
Kungiyar Kirista Ta Najeriya Ta Buƙaci Buhari Ya Janye Tallafin Man Fetur Kafin 2023
A wani labarin, kun ji cewa Kungiyar Kirista ta Najeriya, NCF, gammayar mabiya Katolika da Protestant ta ce ya zama dole gwamnatin tarayyar Najeriya ta jajirce ta ceto kasar daga rushewa ta hanyar cire tallafin man fetur, .
NCF ta ce akwai alamu kwarara da ke nuna cewa idan an cire tallafin man fetur, da aka ce yana lashe kimanin Naira biliyan 250 duk wata, tattalin arzikin zai shiga mummunan hali, Guardian ta ruwaito.
A wani taron manema labarai a Abuja, shugaban NCF, Bishop John Matthew, tare da sauran shugabannin kungiyar, sun ce tallafin man fetur babban kallubale ne da ya kamata a tunkare shi gadan-gadan.
Asali: Legit.ng