Buhari ya fasa zuwa Zamfara: Gwamna Matawalle ya yi martani kan matakin Buhari
- Gwamnan jihar Zamfara ya yi martani bayan da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bayyana fasa zuwa jihar
- An tsara shugaban kasa Muhammadu Buhari zai kai ziyarar jaje jihar Zamfara a yau Alhamis, amma ya fasa saboda dalilai
- Gwamnan ya bayyana rashin jin dadinsa, amma ya ce ya magantu da shugaban kasa Muhammadu Buhari kan ziyarar
Jihar Zamfara - Gwamna Bello Mattawale na jihar Zamfara ya bayyana dage ziyarar da shugaban kasa, Muhammadu Buhari zai kai jiharsa a matsayin wani abu da Allah ya kaddara.
Jaridar Punch ta ruwaito Matawalle yana cewa:
“Mutum na nasa, Allah na nasa. Ina mai bayyana takaicin cewa shugaban kasa Muhammadu Buhari ya dage ziyarar jajantawa jihar Zamfara saboda dagulewar yanayi.
Premium Times ta rahoto cewa, lokacin da yake bayyana dalilin da yasa Buhari bai iso jihar ta Zamfara, gwamna Matawalle ya shaidawa manema labarai a yammacin Alhamis cewa:
“Saboda hazo, shugaban kasa ba zai iya zuwa Zamfara ba.
“A matsayinmu na Musulmi, mun yarda da wannan a matsayin wani abu da Allah ya kaddara.
“Tsaron shugaban mu ya fi sha’awar mu."
Hakazalika, gwamnan ya kuma shaida cewa, ya tattauna da shugaban kasa, inda ya shaida masa nan ba da dadewa ba zai sake sake shirya wata ziyarar a Zamfara.
A cewar Matawalle:
"Duk da haka, na yi magana da shugaban kasa, wanda ya ba ni tabbacin sake tsara ziyarar nan ba da jimawa ba."
Najeriya za ta yi nasara a gwagwaryar da take da matsalolin tsaro, Buhari ya ba da tabbaci
A wani labarin, shugaban kasa Muhammadu Buhari ya sake umurtan rundunar sojojin kasar da sauran hukumomin tsaro da su yi maganin duk wani mutum ko kungiyar da ke yiwa kokarin kawo zaman lafiya, tsaro da daidaituwar kasar zagon kasa.
Buhari ya kuma bayar da tabbacin cewa kasar za ta yi nasara a kan miyagun mutane.
Mai ba shugaban kasa shawara a kan harkokin labarai, Femi Adesina ne ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da ya fitar a shafinsa na Facebook mai taken "Za mu yi nasara a kan miyagun mutane, Shugaba Buhari ya bayar da tabbaci a ziyarar ta'aziyya a Sokoto."
Asali: Legit.ng