An kashe sifetan ‘yan sanda yayin musayar wuta da ‘yan bindiga

An kashe sifetan ‘yan sanda yayin musayar wuta da ‘yan bindiga

  • Sifetan ‘yan sanda, Omolayo Olajide da wasu ‘yan bindiga biyu sun rasa rayukan su a ranar Talata yayin wata musayar wuta tsakanin ‘yan sanda da ‘yan bindiga
  • Musayar wutar ta auku ne a cikin dajin Saala Orile da ke karamar hukumar Yewa ta arewa da ke Jihar Ogun kamar yadda kakakin rundunar ‘yan sandan, Abimbola Oyeyemi ya shaida
  • Sun yi mintuna 20 suna musayar wutar inda da dama ‘yan bindigan suka samu miyagun raunuka sannan ‘yan sanda suka kwace makamai da dama

Jihar Ogun - Sifetan ‘yan sanda, Omolayo Olajide da wasu ‘yan bindiga biyu sun rasu a ranar Talata yayin musayar wutar da ta auku tsakanin ‘yan sanda da ‘yan bindiga, Premium Times ta ruwaito.

An samu bayanai akan yadda harbe-haren ya auku tsakanin ‘yan sanda da ‘yan bindigan a dajin Saala Orile da ke karamar hukumar Yewa ta arewa da ke Jihar Ogun.

Kara karanta wannan

Filato: An shiga firgici yayin da 'yan bindiga suka farmaki jama'a, suka kashe da dama

Sifetan ‘yan sanda ya mutu yayin musayar wuta da ‘yan bindiga
'Yan bindiga sun kashe sufetan yan sanda yayin musayar wuta. Hoto: Premium Times
Asali: Getty Images

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Abimbola Oyeyemi, kakakin rundunar ‘yan sandan Jihar Ogun ya ce bayan sun samu kiran gaggawa a ofishin ‘yan sanda na Ayetoro, Bernard Ediogboyan, ya jagoranci yaran sa da rundunar JSIS zuwa inda ‘yan bindiga suke ta’addanci.

Sun kai minti 20 suna musayar wuta

A cewarsa:

“Bayan ganin ‘yan sandan, ‘yan bindigan suka fara bude musu wuta suma ‘yan sandan suka fara harbin su.
“Bayan kwashe mintuna 20 suna barin wuta, ‘yan bindiga biyu sun rasu yayin da wasu da dama suka tsere da raunuka.”

Premium Times ta ruwaito yadda ya ci gaba da bayanin inda ya ce:

“Abin ban takaicin shi ne yadda sifetan ‘yan sanda ya rasu yayin musayar wutar.”

Kwamishinan ‘yan sanda ya bukaci rundunar ta yi gaggawar kamo wadanda suka kai farmakin

A cewar Oyeyemi, an samu nasarar kwace bindigogin toka uku, harsasai 16, layun tsafi, adda daya, karamar waya daya da kuma wani babur kirar Bajaj mara lamba a jikin shi.

Kara karanta wannan

Zamfara: Jama'a sun fada shagali da murna bayan sojoji sun ragargaza 'yan ta'adda a daji

Kwamishinan ‘yan sanda, Lanre Bankole, ya nuna rashin jin dadin sa akan mutuwar jami’in ‘yan sandan kuma ya ce mutuwar tasa ba za ta tafi a banza ba.

Kwamishinan ya umarci rundunar ta yi gaggawar kamo duk wadanda ke da alhakin kai farmakin don a yanke musu hukunci.

'Yan bindiga sun sace babban limami da wasu mutane 10 yayin da suke sallah a Sokoto

A wani labarin, 'yan bindiga sun sace mutane 11 ciki har da babban limami, Aminu Garba, wanda ke shirin jagorantar mutane yin sallah Juma'a a jam'i a kauyen Gatawa da ke karamar hukumar Sabon Birni a Jihar Sokoto.

An sace limamin tare da wasu mutane uku ne a ranar Juma'a kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.

Maharan sun tare hanyar Sabon Birnin zuwa Gatawa a ranar Asaba, inda suka bindige mutane uku suka kuma sace wasu mutanen bakwai.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164