Da duminsa:Tsohon shugaban majalisar dattawa ya kuduri aniyar gaje kujerar Buhari
- Tsohon sanata, Abubakar Bukola Saraki ya bayyana kudurinsa na tsayawa takarar shugaban kasa a 2023
- Saraki ya bayyana haka ne a yau Larana 26 ga watan Janairu, kamar yadda majiyoyi suka bayyana
- A baya an samu wasu 'yan siyasan Najeriya daga jam'iyyu daban-daban da suka nuna sha'awarsu ta tsayawa takara
Wani rahoton The Nation ya bayyana cewa, tsohon shugaban majalisar dattawa Bukola Saraki ya nuna sha’awar tsayawa takarar shugaban kasa a 2023.
Ayyanawar tasa na zuwa ne bayan tsohon jagoran jam’iyyar APC Asiwaju Bola Ahmed Tinubu; Gwamnan Ebonyi, Dave Umahi, Dan Majalisar Dattawa, Orji Kalu, da tsohon Gwamnan Imo, Rochas Okorocha, suka bayyana tasu aniyar.

Asali: Facebook
Saraki, tsohon Gwamnan Kwara ya ce yana da kyakkyawan tarihi na gudanarwa da gogewa wajen tafiyar da lamurra yadda ake bukata.
An haifi Saraki a ranar 19 ga Disamba, 1962, dan Sanata ne a jamhuriya ta biyu, marigayi Olusola Saraki.
Ziyarar sa a Makurdi
Tun da farko dai dan siyasar ya ziyarci gwamnan jihar Benue, Samuel Ortom a ranar Talata a garin Makurdi, wanda ya kira mutumin kirki a jam'iyyar PDP, inji rahoton jaridar Punch.
Ya ce:
“Jam’iyyar siyasar da ba za ta iya tsara al’amuranta ba, ba ta cancanci ta jagoranci kasar nan ba. Jam’iyyar da ta shirya al’amuranta kuma a shirye take ta jagoranci kasar nan, ita ce PDP”.
A wani labarin, tsohon gwamnan jihar Imo, Sanata Rochas Okorocha, ya bayyana aniyarsa ta tsayawa takarar shugaban ƙasa a zaɓen 2023.
Punch ta rahoto cewa Okorocha ya bayyana haka ne a wata wasika da shugaban majalisar dattawa, Sanata Ahmad Lawan, ya karanta a zaman yau Laraba.
A ranar Litinin, 31 ga watan Janairu, 2022, tsohon gwamnan zai yi jawabi a wurin taron manema labarai na duniya, inda ake sa ran zai yi ƙarin haske kan manufofinsa.
Asali: Legit.ng