Edo: 'Yan ta'adda sun sace bakon haure, sun halaka dan sandan da ke kula da shi
- ‘Yan bindigan da ake zargin masu garkuwa da mutane ne sun sace wani bakon haure da ke aiki a wata ma’aikata a ranar Litinin
- An samu bayanai akan yadda ‘yan bindigan suka fara halaka wani dan sanda da ke kula da lafiyar bakon hauren kafin su sace shi
- Ganau sun ga yadda ‘yan bindigan suka fito daga daji suka fara harbe-harbe ta ko ina kafin su sace shi su tsere dajin da shi
Edo - Wasu ‘yan bindigan da ake zargin masu garkuwa da mutane ne sun sace wani bakon haure da ke aiki da wata ma’aikata a jihar Edo ranar Litinin, Daily Trust ta ruwaito hakan.
An samu bayanai akan yadda ‘yan bindigan suka fara da harbe dan sandan da yake kula da shi yayin da yake aikin a kamfanin Hartland da ke kan titin Idegu-Awain a karamar hukumar Etsako da ke Jihar tukunna suka sace shi.
Ganau sun shaida yadda ‘yan bindigan suka bayyana daga daji suka dinga harbe-harbe ko ta ina daga nan suka halaka dan sandan da ke kula da lafiyar shi sannan suka sace shi suka tsere da shi cikin dajin.
Rahotanni sun nuna yadda daga bisani ‘yan sanda suka zo don daukar gawar zuwa ma’adanar gawa, Daily Trust ta ruwaito.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Wata majiya daga anguwar ta ce yanzu haka Yan Sa Kai suna ta binciken dajikan da ke kusa don nemo inda bakon hauren yake.
Yayin da aka tuntubi jami’in hulda da jama’an rundunar ‘yan sandan jihar, ya ce bai riga ya samu bayanai dangane da lamarin ba amma ya yi alkawarin sanar da manema labarai idan ya samu rahoton.
Nasara: Soji sun bankado farmakin 'yan ta'adda, sun ceto dan siyasa da iyalinsa a Zamfara
A wani labari na daban, sojoji tare da taimakon 'yan sa kai a daren Asabar sun ceto wani dan siyasa da iyalansa bayan musayar wuta da suka yi da 'yan ta'addan inda aka kashe 'yan ta'adda masu yawa.
Majiyoyi daga Gusau, babban birnin jihar Zamfara, sun tabbatar wa da Premium Times cewa, an sace dan siyasa Aminu Adamu a gidan sa da ke kwatas din Mareri da ke birnin.
Adamu wanda aka fi sani da Papa, shi ne manajan daraktan hukumar sufuri ta jihar Zamfara kuma makusancin Gwamna Bello Matawalle.
Wani mazaunin yankin mai suna Zayyanu Muhammad, ya sanar da cewa 'yan ta'addan sun bayyana a babura inda kai tsaye suka tsinkayi kwatas din Mareri inda Adamu da iyalansa su ke.
Asali: Legit.ng