'Yan sanda sun yi ram da hatsabibin ɓarawo dauke da IPhones 16, kwamfuta da wasu kayayyaki a Oyo

'Yan sanda sun yi ram da hatsabibin ɓarawo dauke da IPhones 16, kwamfuta da wasu kayayyaki a Oyo

  • Jami'an yan sanda a Jihar Oyo sun yi nasarar kama wani barawo mai shekaru 23 da ya saba balle gidajen mutane yana yi musu sata
  • An kama shi ne a gidansa dauke da wayoyin IPhones 16, kwamfuta laptop guda biyu, na'urar jin magana kunne na earpiece da jaka da sauransu
  • Wanda ake zargin ya amsa laifin da ake tuhumarsa da shi na balle wani shago inda ya sace kayan da nufin ya sayar sannan ana zurfafa bincike don gano abokan aikinsa

Jihar Oyo - Yan sanda a Jihar Oyo sun kama wani hatsabibin barawo mai shekaru 23 a jihar da wayoyin IPhones 16 da laptop kwamfuta biyu da wasu kayayyakin, rahoton Premium Times.

Kwamishinan yan sandan jihar, CP Ngozi Onadeko, ta bayyana hakan cikin wata takarda da kakakin rundunar, SP Adewale Osifeso ya fitar a ranar Talata a Ibadan.

Kara karanta wannan

Dubun wani matashin saurayi da ake zargi da kashe budurwarsa ya cika

'Yan sanda sun kama hatsabibin barawo da IPhones 16, kwamfuta da wasu kayayyaki
'Yan sanda sun kama hatsabibin barawo da IPhones 16 da kwamfuta da wasu kayayyaki a Oyo. Hoto: Premium Times
Asali: Twitter

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Ms Onadeko ta ce jami'an yan sanda na yankin Fedele, sun kama wanda ake zargi da hannu a satar da aka aikata a Choice Plaza, misalin karfe 8 na dare a ranar Disamba 28 a Ibadan inda aka sace wayoyi da kayan da kudinsa ya fi N2,000,000.

Ta ce bincike mai zurfi da jami'an rundunar suka yi ne ya yi sanadin kama wanda ake zargin kamar yadda ya zo a rahoton na Premium Times.

Kwamishinan ta ce an binciko wanda ake zargin an kuma kama shi da kayan sata da suka hada da IPhones 16, farin earpiece, air pod 1, kwamfuta kirar Sony Vio da Dell sai kuma bakar jaka.

Wanda ake zargin ya amsa laifinsa a hannun yan sanda

Ms Onadeko ta ce binciken da suka fara yi a yanzu da bayanai daga bakin wanda ake zargin sun nuna ya balle shagon sayar da wayoyin a Choice Plaza, Challenge, Ibadan da nufin ya sace kayan ya sayar.

Kara karanta wannan

Yadda yunkurin zawarcin Jonathan, a ba shi takara a APC ya sha ruwa tun kafin a kai 2023

Ta ce ana zurfafa bincike domin gano sauran wadanda suke aiki tare da wanda ake zargin.

CPn ta shawarci mazauna Jihar Oyo su cigaba da bawa rundunar hadin kai ta hanyar bada bayanai masu amfani a kan lokaci don taimakawa wurin tabbatar da zaman lafiya a jihar.

Katsina: 'Yan sanda sun kama wani da ke yaudarar mata ya kwana da su a otel ya kuma sace musu waya da kuɗi

A wani labarin, jami'an yan sanda a Jihar Katsina sun kama wani mutum mai shekaru 31 da ake zargin yana amfani da intanet wurin yaudarar mata yana kwanciya da su a Kano, Vanguard ta ruwaito.

An shaida wa manema labarai cewa wanda ake zargin, Usama Tijjani, mazaunin Daurayi Quaters ne a karamar hukumar Gwale a Jihar Kano.

Yan sandan suna zarginsa da:

"Kai 'yan mata otel domin ya kwanta da su sannan ya yaudara su ya sace musu kayayyakin su masu muhimmanci".

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164