Boko Haram: 'Yan ta'adda sun kone gine-gine 110 a Chibok, Zulum ya je ziyarar jaje
- Gwamnan jihar Borno ya kai ziyarar jaje a yankin Chibok bayan da Boko Haram suka kai sabon hari
- An hallaka mutane da dama tare da sace wasu a wani sabon harin 'yan ta'addan Boko Haram a yankin
- Zulum ya tattauna da shugaban yankin, ya kuma nemi a bashi rahoto kan abin da ya faru domin neman mafita
Chibok, Borno - Gwamnan jihar Borno, Babagana Zulum, ya ziyarci karamar hukumar Chibok domin jajantawa mazauna kan hare-haren da aka kai wasu kauyuka uku a yankin.
Wasu da ake zargin mayakan Boko Haram ne sun kai hari a Kawtakare, Korohuma da Pemi a karamar hukumar, The Cable ta ruwaito.
Rahotonni sun tattaro mutuwar mutane hudu, tare da kona gidaje 110 da maharan suka yi, kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.
Gwamnan wanda ya ziyarci yankin ranar Litinin ya kuma gana da iyalan mata 22 da maza biyu da aka ce an yi garkuwa da su a yayin harin.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
An rahoto Zulum na cewa:
“Muna nan garin Chibok ne domin mu jajanta muku, iyalan ‘yan uwanmu mata da ‘yan uwanmu maza da aka sace da kuma ‘yan uwanmu hudu da ‘yan ta’addan Boko Haram suka kashe a wadannan munanan harin. Muna taya ku jimami kuma muna addu'ar kada wannan barna ta sake faruwa."
Umar Ibrahim wanda ya yi wa gwamnan bayanin hare-haren, ya ce baya ga mutane 24 da aka yi garkuwa da su, maharan sun kashe mutane uku a lokacin da suka kai hare-hare daban-daban a yankunan uku.
Ya ce an kona gine-gine guda 110 da suka kunshi gidaje 73, shaguna 33 da coci-coci hudu tare da motoci takwas da babura uku.
Zulum ya ba da umarnin a mika masa rahoton tantancewa da ke kunshe da duk barnar da maharan suka yi a yankunan uku.
Ya kuma yabawa shugaban bisa yadda ya jagoranci jagoranci.
A kalaman Zulum:
“Ina yaba wa kokarin shugaban karamar hukumar, domin duk da karancin kayan aiki, ya yi iyakacin kokarinsa wajen ganin an samar da romon dimokradiyya a Chibok."
Gwamnan ya ce kimanin kananan hukumomi hudu na Biu, Askira, Chibok da Damboa ne suka fuskanci hare-hare daga ‘yan tada kayar bayan a ‘yan kwanakin nan.
Ya ce gwamnatinsa ba za ta yi kasa a gwiwa ba wajen baiwa jami’an tsaro karin tallafi domin tunkarar kalubalen.
Bayan ganawa da iyalan wadanda abin ya shafa a garin Chibok, gwamnan ya gana da shugabannin hukumomin tsaro inda suka tattauna gibi da hanyoyin inganta tsaro a cikin al’umma.
Buhari a Borno a watan Disambar da ta gabata
A wani labarin, Shugaba Muhammadu Buhari ya dira Maiduguri, babban birnin jihar Borno, domin ziyarar aiki ta kwana daya mintuna kadan bayan 'yan Boko Haram sun harba roka cikin filin jirgin sama na Maiduguri, Daily Trust ta ruwaito.
Manyan ma'aikatan gwamnati sun yi wa Buhari rakiya zuwa Borno, jirginsa ya dira a Maiduguri misalin karfe 11.45 na safiyar yau Alhamis.
Gwamnan Jihar Borno, Farfesa Babagana Zulum, ya na filin jirgin tare da dukkan shugabannin tsaro, da suka isa jihar domin tarbar Buhari.
Asali: Legit.ng