Ni na yi mata komai: Saurayin da budurwarsa ta ki amincewa ta aure shi ya magantu cikin hawaye

Ni na yi mata komai: Saurayin da budurwarsa ta ki amincewa ta aure shi ya magantu cikin hawaye

  • Wani dan Najeriya wanda budurwarsa ta zuba masa kasa a ido ta hanyar kin yarda da bukatarsa na son ta aure shi ya magantu a kan alakarsa da matashiyar
  • Mutumin wanda ke gyaran wayoyi a Abuja ya bayyana cewa abun da matukar ciwo ganin cewa budurwar da ya shafe tsawon shekaru hudu yana soyayya ita za ta iya yi masa haka
  • Cikin hawaye saurayin ya bayyana dalilin da yasa ya kunyata matashiyar bayan ya kama ta tare da wani mutum a wajen taro

Mutumin da budurwa ta tozarta a yayin da ya nemi ta aure shi ya bayyana wasu sirrika game da soyayyar tasu wacce ta yi tsami a yanzu.

Bayan rashin nasara a bukatar auren, mutumin wanda yake mazaunin Abuja ya haifar da yar dirama a wajen wani bikin zagayowar ranar haihuwa wanda a nan ne ya ga budurwar tare da sabon saurayinta.

Kara karanta wannan

N13k ne albashinmu: Sanata ya bayyana yadda ake biyan sanatoci a 1999

Dalilin da yasa ya haifar da yar dirama

A wani sabon bidiyo inda a ciki yake bayanin dalilinsa na aikata abun da ya yi, mai gyaran wayoyin ya bayyana cewa ya shafe tsawon shekaru hudu yana soyayya da budurwar.

A cewar mutumin da ke cike da bacin rai, ya halarci wani bikin zagayowar ranar haihuwa amma ga mamakinsa sai ya gano budurwar tare da sabon saurayinta.

Ni na koya mata komai: Saurayi ya tada rikici saboda budurwarsa ta ki amincewa ta aure shi
Ni na koya mata komai: Saurayi ya tada rikici saboda budurwarsa ta ki amincewa ta aure shi Hoto: @instablog9ja
Asali: Instagram

Ba iya nan yaudarar ta tsaya ba, mutumin ya ce ya lura cewa sabon saurayin tsohuwar budurwar tasa yana sanye da wani farin riga da agogo wadanda suke mallakinsa ne.

Hakan ya fusata shi yayin da ya tunkari matar don karbar kayansa.

Yayin da yake kokarin mayar da hawayen idanunsa a lokacin da yake magana, dan kasuwar ya bayyana cewa shi ya dauki dawainiyar makarantar ta, takardu da dukkan bukatunta na kudi.

Kara karanta wannan

Yaudara: Bayan wata ɗaya da saurayi ya bai wa mahaifiyar ta ƙoda, ta yi wufff ta aure wani

Ya caccaki masu amfani da yanar gizo da suka aibata shi ba tare da jin cikakken labarin ba.

Kalli bidiyon a kasa:

Yan Najeriya sun yi martani

@odinny ya ce:

"Gayen nan na cike da bacin rai. Allah ya dawo da shekarun da ya bata. Ya zuba dukka jarinsa don kula da ita kuma ga dukkan alamu ta yi amfani da shi ne saboda tana ganin bai kai ajinta ba. rayuwa kenan. Ya ci buri a kanta. Ina Masa fatan samun waraka da ci gaba da rayuwa. Kallon wannan akwai radadi."

@asiwajulerry ya ce:

"Da wahala mutum ya kula da tallafawa macen da yake so a wannan zamanin da dukkan abubuwan nan da mutum ke karantawa a yanar gizo."

@wallpaperplace ta rubuta:

"Ya dauki nauyin makarantarta...Ina jin radadinka faaa. Sun kara yaji a yaudarar da suka yi maka."

Mawaki ya yi tsokaci kan budurwar da ta rude, ta na neman zabi tsakanin saurayi da kuma karatu kasar waje

Kara karanta wannan

An dakatar da dagaci kan yi wa budurwa auren dole, cin zarafin mahaifin ta da nada mata duka

A gefe guda, shahararren mawakin nan na Najeriya, Ric Hassani, ya yi martani ga budurwar da ke tunanin wanda za ta zaba tsakanin saurayinta da kuma tallafin da ta samu na yin karatu a kasar waje.

A ranar Asabar ne Rita Orji, wata yar Najeriya mai bincike da ke zama a Canada, ta je shafinta na Twitter domin bayyana wani sako da ta samu a akwatin sakonta na gmail daga wata budurwa mai shekaru 22.

A cewar Orji, budurwar ta samu tallafi kwanan nan domin tafiya yin digir na biyu a kasar waje.

Asali: Legit.ng

Online view pixel