Yan ta'adda sun bindige 'yan sanda har Lahira, sun yi awon gaba da babban ɗan kasuwa a Jigawa
- Wasu yan bindiga sun kutsa gidan wani mutumi ɗan kasuwa a garin Kwalam dake jihar Jigawa, sun yi awon gaba da shi
- Hukumar yan sandan jihar ta bayyana cewa ta rasa yan sanda guda biyu a kokarin su na daƙile harin bayan samun rahoto
- Kakakin yan sanda yace jami'ai na cigaba da kokarin ceto wanda aka sace tare da kame masu hannu kan harin
Jigawa - Rundunar yan sanda reshen jihar Jigawa ta tabbatar da cewa wasu miyagun yan bindiga sun harbe yan sanda biyu a karamar hukumar Taura.
Jaridar The Nation ta rahoto cewa yan ta'addan sun kutsa cikin gidan wani ɗan kasuwa, suka yi awon gaba da shi.
Kakakin hukumar yan sanda na jihar, shi ne ya tabbatar da faruwar lamarin ga hukumar dillancin labarai ta ƙasa (NAN) a Dutse ranar Litinin.
Shiisu ya bayyana cewa lamarin ya faru ne yayin da yan bindigan suka kutsa gidan wani, Alhaji Ma'aru, Abubakar, dake garin Kawalam, suka yi awon gaba da shi.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Daily Trust ta rahoto Kakakin yan sandan yace:
"A ranar 23 ga watan Janairu, 2022, mun samu kiran gaggawa da misalin ƙarfe 1:30 na dare cewa wasu yan bindiga sun kai hari garin Kwalam dake ƙaramar hukumar Taura."
"Nan take bayan samun rahoton, muka tura tawagar jami'an yan sanda zuwa garin. Da isar su, suka fara musayar wuta da maharan, har suka tsere."
"Jami'ai biyu, ASP Anas Usaini da Sunusi Alhassan sun rasa rayuwarsu a kusa da motar sintiri, wacce yan bindiga suka ƙone ta kurmus."
Wane matakin hukumar yan sanda ta ɗauka bayan haka?
Mista Shiisu ya tabbatar da cewa tuni hukumar yan sanda ta kaddamar da bincike kan lamarin da kuma kamo maharan.
"Binciken da muka yi na farko, ya nuna cewa yan ta'addan sun farmaki gidan Alhaji Ma'aru Abubakar, kuma suka yi gaba da shi."
Ya ƙara da cewa yan sanda sun bazama neman maharan domin ceto mutumin da kuma kame yan ta'addan.
A wani labarin kuma Miyagun yan bindiga sun kai mummunan hari kan mutanen ƙauye, Sun bindige Manajan gidan mai da yaronsa
Wasu yan ta'adda da ake zargin Fulani makiyaya ne sun halaka mutum biyu a wani sabon hari da suka kai ƙauyen jihar Ondo.
Yan bindigan sun buɗe wa Manajan gidan man Fetur da yaronsa ɗaya wuta, kuma dukka mutum biyun sun mutu zuwa safiyar Litinin.
Asali: Legit.ng