Yan bindiga na kwantawa da matanmu da yayanmu mata saboda rashin biyan harajin N2m – Mazauna Zamfara

Yan bindiga na kwantawa da matanmu da yayanmu mata saboda rashin biyan harajin N2m – Mazauna Zamfara

  • Al'umman garuruwan yankin Kurya Madaro a karamar hukumar Kaura Namoda da ke jihar Zamfara suna tserewa daga gidajensu don tsira daga farmakin yan bindiga
  • An tattaro cewa mazauna yankin sun koka kan cewa yan bindigan sun koma yin lalata da matansu da yayansu mata saboda sun gaza biyan harajin da suka daura masu
  • Maharan dai sun daura masu biyan harajin naira miliyan 2 kowannensu idan har suna son zama lafiya

Zamfara - Mazauna garuruwa biyar da ke karkashin yankin Kurya Madaro a karamar hukumar Kaura Namoda da ke jihar Zamfara sun tsere daga gidajensu bayan yan bindiga sun koma yiwa matansu da yayansu mata fyade saboda rashin biyan kudin harajin da suka daura masu.

An tattaro cewa mazauna garuruwan da abun ya shafa sun zabi tserewa don tsira daga ci gaban hare-hare bayan sun gaza biyan yan bindiga naira miliyan 2 da suka daurawa kowannensu.

Kara karanta wannan

Dare daya: Shekaru 18 basu kwana a kan gado ba saboda talauci, an canza rayuwarsu

Yan bindiga na kwantawa da matanmu da yayanmu mata saboda rashin biyan harajin N2m – Mazauna Zamfara
Yan bindiga na kwantawa da matanmu da yayanmu mata saboda rashin biyan harajin N2m – Mazauna Zamfara Hoto: Premium Times
Asali: UGC

A wata hira da jaridar Tribune, wani mazaunin Balankadi, Malam Rabi'u Abubakar, wanda ke samun mafaka a wajen garin, ya ce yan bindigar sun ce lallai sai sun biya naira miliyan 2 kafin su barsu su samu zaman lafiya.

Abubakar ya ce al'umman garinsa sun yi nasarar tattara naira miliyan 1.5 ne wanda suka gaggauta mika shi ga yan bindigar amma kudin bai isa sama masu yanci daga maharan ba.

Ya ce:

"Maharan suna haikewa matanmu, yayanmu mata da kannenmu a duk lokacin da suka kawo farmaki kauyen da dare ko da rana. Sannan suna kashe duk mutumin da yayi kokarin kawo shamaki. Wannan kari ne ga sace-sacen da suke yi a shagunan abincinmu da kuma cinnawa gidajenmu wuta a wasu lokutan."

Abubakar ya koka kan abun da ya kira ga rashin jami'an tsaro a garuruwan, lamarin da a cewarsa ya ba yan bindiga damar jan ragamar yankin gaba daya.

Kara karanta wannan

Tsagwaron barna: Wasu miyagun 'yan bindiga sun fille kan tsoho mai shekaru 65

Kwamishinan yan sandan jihar, Ayuba Elkana, a wani taron manema labarai da aka yi a kwanaki, ya bayyana cewa yan sanda da sauran hukumomin tsaro sun jajirce don dawo da zaman lafiya mai dorewa a jihar.

Ku biya mu haraji ko ku dandana kudarku: Yan bindiga sun aika wasiku ga kauyukan Zamfara 9

A wani labarin, yan bindiga da ke ta'asa a dajin Gando a karamar hukumar Bukkuyum na jihar Zamafara sun aika wasika zuwa wasu garuruwa tara inda suka nemi su biya harajinsu ko kuma su fuskanci mummunan hari.

Hakan na zuwa ne yan makonni bayan kisan kiyashin da yan bindiga suka yi wa a kalla mutane 200 a kananan hukumomin Bukkuyum da Anka.

A wannan harin, yan bindigar sun kona kauyuka biyar, suka kashe mazauna garin da dama sannan suka yanka gawarwakinsu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng