Osun: Kwamishina Musulmi ya dauka nauyin gina sakateriyar CAN
- Kwamishinan kudi na jihar Osun, Bola Oyebamiji, ya gina wa kungiyar Kiristoci ta kasa, CAN, reshen karamar hukumar Irewole sakateriya
- Ba ginin ba ne abun mamaki, Oyebamiji Musulmi ne kuma ya na da sarautar Balogun Musulumi na kasar Ikire da ke jihar
- Shugaban CAN, Samson Ayokunle, ya bayyan jin dadin sa da kuma yabawa ga Oyebamiji kan kokarin sa da kuma hakuri da addinin da ba nasa ba
Osun - Bola Oyebamiji, kwamishinan kudi na jihar Osun kuma mai sarautar Balogun Musulumi of Ikireland, ya dauka nauyin ginin sakateriyar kungiyar Kiristoci ta kasa, CAN a karamar hukumar Irewole da ke jihar.
A yayin kaddamar da sabon ginin sakateriyar a ranar Alhamis, Samson Ayokunle, shugaban CAN, ya jinjina wa Oyebamiji kan kokarin sa, kuma ya yi kira ga 'yan Najeriya da su rungumi hakuri da addinan da ba nasu ba.
Kamar yadda The Punch ta ruwaito, shugaban CAN ya nuna murnar sa kan yadda kwamishinan ya nuna misalin da ya dace a yi koyi.
“Bola Oyebamiji mutum ne da ke da kusanci da iyalai na a sama da shekaru ashirin kuma hakan ya ke har yanzu," Ayokunle ya ce.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
“Mutum ne nagari kuma mai hakuri ga kowa, ba ya duban addini. Na san yadda ya ke dagewa wurin aikin Ubangiji wurin gina majami'u da masallatai.
"Dole ne in ce abun jinjna ne. Wannan a koda yaushe na ke kira a kai - alaka mai kyau tsakanin dukkan addinai. Wannan ne abin da Ubangiji ke so. Wannan ce kadai hanyar da za mu samu zaman lafiya a kasar nan. Abun farin ciki ne sanin cewa Irewole ne ya dauka nauyin wannan aiki, hakan ya na sanya ni farin ciki sosai."
Ayokunle ya yi kira ga 'yan Najeriya da su gane cewa kasar nan za ta yi dadin zama ne ga kowa idan akwai zaman lafiya da hakuri da juna, TheCable ta ruwaito.
Ko shaiɗan ba zai faɗi abubuwan da ake yaɗawa ba, Mummy GO ta ce lalata bidiyoyin ta aka yi
A wani labari na daban, Funmilayo Adebayo, fitacciyar faston Najeriya wacce aka lakaba wa suna Mummy GO, ta yi ikirarin cewa bidiyoyin da ake yadawa kan da'awarta na hankada mutane wuta duk shirya su aka yi.
Mummy GO ta zama abun magana a kafafen sada zumunta kan yadda wa'azin ta da da'awoyin ta ke hankada mutane wuta kai tsaye. A tattunawar faston da BBC, ta yi magana kan yadda ake yin martani daban-daban kan koyarwarta.
Ta ce ko shaidan dai ba zai yi wasu daga cikin tsokacin da ake alakantawa da ita ba a kafafen sada zumunta.
Asali: Legit.ng