Me yasa ka kashe ta: Mahaifiyar Haneefa da aka yiwa kisan gilla ta farmaki makashin 'yarta

Me yasa ka kashe ta: Mahaifiyar Haneefa da aka yiwa kisan gilla ta farmaki makashin 'yarta

  • Yayin da suka isa hedkwatar 'yan sanda, mahaifiyar Hanifa Abubakar da aka yiwa kisan gilla ta farmaki makashin diyarta
  • Hakan ya faru ne a yau Juma'a yayin da aka kawo wadanda suka sace yarinyar suka hallaka ta a kwanakin baya
  • Malamin Hanifa Abubakar ne ya sace ta, ya ajiye ta a gidansa na wani lokaci kafin daga bisani ya yi mata kisan gilla

Kano - Daily Trust ta ruwaito cewa, an yi rikici a hedikwatar rundunar ‘yan sandan jihar Kano, yayin da Fatima Maina, mahaifiyar Haneefa Abubakar, ‘yar shekara biyar da aka ce malaminta ya kashe, ta hango mutumin da ya yi garkuwa da diyarta.

A baya an ruwaito yadda aka kama Abdulmalik Tanko, shugaban makarantar Noble Kids Nursery and Primary School da ke Kawana, Kano, dangane da lamarin.

Kara karanta wannan

Na san zafin haihuwa: Makashin 'yar makaranta Hanifa ya bayyana adadin 'ya'yansa

Tun a watan Disamba ne aka yi garkuwa da Haneefa, kuma masu garkuwar suka bukaci a biya ta Naira miliyan 6 a matsayin fansa.

Mahaifiyar Haneefa ta farmaki makashin diyarta
Yanzu-Yanzu: Mahaifiyar Haneefa da aka yiwa kisan gilla ta farmaki makashin 'yarta | Hoto: dailynigerian.com
Asali: UGC

Yayin da yake kokarin karbar wani bangare na kudin fansan, jami’an tsaro sun cafke Tanko da wasu da ake zargi.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

A ranar Juma’a, iyayen yarinyar da aka kashe da wadanda ake zargin sun hadu a hedikwatar ‘yan sandan Kano.

Iyayen yarinyar su ne suka fara isa wurin. Daga baya sai ‘yan sanda suka kawo Tanko da sauran wadanda ake zargin.

Nan take da Fatima ta hango Tanko, sai ta farmake shi, tana yi masa ruwan mari da kullin naushi a lokacin da take neman dalilin da ya sa ya kashe diyarta.

An ci gaba da rikicin na dan lokaci har sai da 'yan sanda suka fatattaki suka shiga tsakani.

Kara karanta wannan

Shugaban makarantar su Hanifa ya magantu: Da gubar beran N100 na kashe ta

Legit.ng Hausa ta tuntubi kawun Hanifa don jin ko an ba da sauran abin da ya rage daga gawarta, ya dauki wayar amma bai yi magana ba sannan ya kashe wayan.

Wasu miyagun 'yan bindiga sun fille kan tsoho mai shekaru 65

An fille kan wani mutum tsoho mai shekaru 65 a Ubudom Atta da ke karamar hukumar Njaba a jihar Imo.

Bayan fille kan mutumin mai suna Nnoruoka Onyeokwu, an nuna kan nasa a makarantar firamare da ke unguwar.

Yankin Njaba dai ya sha fama da tashe-tashen hankula da kashe-kashe tun shekarar da ta gabata.

Wakilin jdaridar Daily Trust ya tattaro cewa an kai wa mamacin hari ne a gidansa da daddare inda mutanen kauyen suka farka washegari sai suka hangi kansa a rataye akan wata bishiya a harabar makaranta.

A wani labarin, wasu tsagerun yan bindiga sun farmaki wurin Jana'iza a Ezinifitte, karamar hukumar Nnewi South, jihar Anambra, inda suka tarwatsa mutanen da suka halarci wurin.

Kara karanta wannan

Yadda Shugaban makaranta ya sace dalibarsa kuma ya kasheta a jihar Kano

Daya daga cikin bakin da suka halarci jana'izar, wanda ya zanta da Daily Trust yace, Jana'izar ta kare babu shiri, bayan maharan sun mamaye yankin.

Mutumin, wanda ya bukaci a sakaya sunansa, yace yan bindigan sun kai harin ne bayan samun labarin wani babban mutum a yankin yana bikin birne yar uwarsa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.