Sarkin Musulmi: Rashin tsaro shine matsalar kasar nan, shi yasa muka gagara ci gaba
- A yau ne sarkin musulmi ya tattauna da wata gidan jarida kan abubuwan da suka shafi ci gaban kasar nan
- Ya yi tsokaci da yawa kan abubuwan da ya kamata shugabanni su sanya a gaba domin kasar nan ta ci gaba
- Ya bayyana cewa, babban abin da ke gaban kasar nan shine matsalar tsaro, domin matsalar za ta iya hana kasar ci gaba
Abuja - Sarkin musulmi na Sokoto, Alhaji Muhammadu Sa’ad Abubakar III ya bayyana yadda matsalolin tsaro suka zama babbar matsala ga Najeriya.
Ya bayyana haka ne a wani taron tattaunawa ta musamman da jaridar Daily Trust ta safiyar yau Alhamis.
Alhaji Sa'ad, ya kuma bayyana abubuwan da ake bukata daga shugabannin kasar nan, inda yace ba zai yiwu kasar ta ci gaba ba a hannun shugabanni masu son kai.
Legit.ng ta sanya ido kan tattaunawar, inda sarkin musulmin ke tsokaci kan yadda tsaro ke da muhimmaci ga ci gaban al'umma.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
A cewarsa:
"Idan babu tsaro, ba za mu ci gaba ba."
Da yake magana kan abin da ya kamata a mayar da hankali a kai, ya bayyana cewa:
"Na fi damuwa da rashin tsaro domin shi ne babban shinge ga kowane bangaren tattalin arziki a duniya."
Idan babu tsaro bautar Allah ma ba za ta yiwu ba
Hakazalika, ya kuma jaddada dogewarsa kan yiwa kasar fatan alheri da tuni ga shugabanni kan abin da ke kansu na ciyar da kasa gaba, inda yake cewa:
"Ba za mu iya gajiya ba kuma kada mu gaji da maganar zaman lafiya. Idan babu tsaro, ba za ku ci gaba ba, ba za ku iya bauta wa Allah ba.
Ya kuma yi bayanin cewa, shugabanni masu son kai ba za su kai kasar ga tudun mun tsira ba, don haka akwai bukatar a jawo hankalin shugabanni su zama masu kyautatawa mabiyansu.
"Ba za ka iya zama shugaba ba idan kana da son kai. A ko da yaushe za mu ke jawo hankalin shuwagabannin mu wajen kyautatawa."
A wani labarin daban, gwamnoni 36 na tarayyar Najeriya sun amince su tattauna da shugabannin kungiyoyin NLC na ‘yan kwadago da na ‘yan kasuwa watau TUC.
Jaridar Daily Trust ta ce gwamnonin jihohin za su yi wannan zama ne a dalilin shawarar da suka ba gwamnatin tarayya na cewa a kara farashin litar fetur.
Shugaban kungiyar gwamnoni na kasa, Dr. Kayode Fayemi ya zanta da manema labarai bayan wani zama da gwamnonin suka yi a birnin tarayya Abuja.
Asali: Legit.ng