Yanzu-Yanzu: Buhari ya sauka a Kaduna bayan dawowa kai tsaye daga Gambiya
- Shugaba Muhammadu Buhari ya dawo gida Najeriya bayan hallartar taron rantsar da Shugaba Adama Barrow a Gambiya a karo na biyu
- Sai dai ba Abuja Shugaban kasar ya wuce ba don zuwa fadarsa ta Villa, ya fara yada zango ne a Jihar Kaduna inda zai yi kwana biyu don kaddamar da wasu ayyuka
- Gwamna Nasir El-Rufai da manyan mukkaraban gwamnatin Jihar Kaduna sun fito sun yi wa Shugaba Buhari tarba ta ban girma a lokacin da ya iso cikin dare
Jihar Kaduna - Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya dira a Jihar Kaduna domin ziyarar aiki na kwana biyu a Jihar, Daily Trust ta ruwaito.
Ana sa ran zai kaddamar da wasu ayyuka da Gwamnan Jihar Kaduna, Mallam Nasiru El-Rufai ya yi.
'Dan marigayi Abacha na shirin shiga APC ne? Babban Sanatan APC ya magantu, ya wallafa hotunansu tare
Shugaban kasar ya iso Kaduna ne daga Banjul, Kasar Gambia, inda ya hallarci taron rantsar da Shugaba Adama Barrow, kan mulki karo na biyu.
Gwamnan Jihar Kaduna El-Rufai da wasu manyan jami'an Gwamnatin Kaduna ne suka tarbe shi, wasu mintuna kadan da suka gabata.
Daily Trust ta ruwaito cewa ana sa ran Buhari zai kaddamar da wasu ayyukan raya birane da wasu ayyukan a garuruwan Kafanchan, Kaduna da Zaria a Jihar ta Kaduna daga ranar Alhamis zuwa Juma'a.
2023: Manya masu son satar dukiyar talakawa ne ba su son a sake samun wani Buharin, Garba Shehu
A wani labarin daban, Fadar Shugaban Kasa ta ce manyan mutane masu aikata rashawa ne ba su son a sake samun 'wani Buhari' a Najeriya saboda wata manufarsu na gina kansu, Daily Trust ta ruwaito.
Mai magana da yawun Shugaba Muhammadu Buhari, Garba Shehu, cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Talata, ya ce zai yi wahala a samu wani shugaba da zai iya zarce irin ayyukan da Buhari ya yi.
Ya yi bayanin kan dalilin da yasa Buhari ba zai 'bari a cigaba da yadda ake harka' a kasar ba a karkashin gwamnatinsa.
Asali: Legit.ng