Da Dumi-Dumi: Gwamna Aminu Tambuwal na Sokoto ya yi babban rashi a cikin iyalansa

Da Dumi-Dumi: Gwamna Aminu Tambuwal na Sokoto ya yi babban rashi a cikin iyalansa

  • Allah ya yi wa Wazirin Tambuwal, Muhammad Bello, rasuwa, wanda yake babban yayan gwamna Aminu Tambuwal na Sokoto
  • Gwamna Aminu Tambuwal, ya sanar da rasuwar yayan nasa da yammacin Talata, za'ayi Jana'iza da safiyar Laraba
  • Kafin mutuwarsa, Marigayi Bello, shi ne ya gaji sarautar Wazirin Tambuwal, bayan rasuwar mahaifinsu shekara 37 da suka wuce

Sokoto - Gwamna Aminu Waziri Tambuwal na jihar Sokoto, ya yi rashin yayansa, Muhammad Bello, ranar Talata, kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.

Kafin rasuwar yayan gwamnan, Marigayi Bello, shi ne ke rike da sarautar Wazirin Tambuwal dake jihar Sokoto.

Marigayin shi ne ya gaji mahaifin su, Alhaji Umaru Waziri Usman, wanda Allah ya yi wa rasuwa shekaru 37 da suka shuɗe. Kuma shine babba a cikin iyalansa.

Kara karanta wannan

Mutum daya ya mutu sakamakon gardama kan Chelsea da Barcelona a Katsina

Gwamna Aminu Tambuwal na jihar Sokoto
Da Dumi-Dumi: Gwamna Aminu Tambuwal na Sokoto ya yi babban rashi a cikin iyalansa Hoto: dailypost.ng
Asali: UGC

Gwamna Tambuwal ya sanar da rasuwar

Da yake sanar da wannan babban rashin, Gwamna Tambuwal na jihar Sokoto, ya nuna damuwarsa tare da miƙa dukkan lamari ga Allah (SWT).

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Gwamnan yace:

"Tare da miƙa dukkan lamarin mu ga Allah (SWT), ina mai sanar da rasuwar babban yayan mu, Alhaji Muhammadu Bello, Wazirin Tambuwal."
"Marigayin wanda ya kai shekaru tsakanin 80-90, ya rasu ne ranar Talata da yamma, kuma shi ne Wazirin Tambuwal na tsawon shekaru 37, bayan ya gaji mahaifin mu, Alhaji Umar Waziri Usmanu."
"Za'a gudanar da Jana'izarsa kamar yadda Addinin mu Addinin Musulunci ya koyar, da safiyar yau Laraba a garin Tambuwal."

Gwamnan ya kuma yi Addu'a, Allah ya gafarta wa mamacin, ya yafe masa kurakuransa, kuma yasa Aljanna ta zama makoma a gare shi.

A wani labarin na daban kuma Gwamna mai jiran gado na shirin kafa kwamitin shirya Jarabawa da Intabiyu ga mutanen da zai naɗa a gwamnatinsa

Kara karanta wannan

Kotun afil ta zabi ranar zama kan shari'ar dake tsakanin tsagin APC na Shekarau da Ganduje

Ga dukkan alamu sai ka tsallake jarabawa da kuma Intabiyu ta baki da baki kafin ka shiga sabuwar gwamnatin jihar Anambra.

Wasu alamu masu ƙarfi daga bakin makusantan gwamna mai jiran gado, Farfesa Soludo, na nuna za'a kafa kwamitin tantance waɗan da za'a naɗa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262