Kebbi: Rayuka 15 ne suka salwanta a farmakin ƴan ta'adda, Jami'ai

Kebbi: Rayuka 15 ne suka salwanta a farmakin ƴan ta'adda, Jami'ai

  • Hukumomi sun sanar da cewa rayuka 15 ne suka salwanta a mummunan farmakin da 'yan ta'adda suka kai jihar Kebbi
  • Kamar yadda rundunar 'yan sandan jihar ta tabbatar, an rasa ran dan sanda daya yayin da sojoji 2 tare da farar hula 13 suka rasu
  • Miyagun 'yan ta'addan sun kai farmakin ne a yankin Danko da ke karamar hukumar Wasagu ta jihar Kebbi a ranar juma'a da ta gabata

Kebbi - A ƙalla mutane 16 ne suka rasa rayukan su a ranar Juma'ah yayin da wasu waɗanɗa ake zargi da zama ƴan bindiga suka kai hari Danko ƙaramar hukumar Wasagu dake jihar Kebbi.

Mai magana da yawun ƴan sandan jihar, Nafi'u Abubakar, yace sojoji biyu, ɗan sanda 1 da mazauna yankin 13 ne suka rasa rayukansu yayin harin da aka kai kauyen Dankade, Premium Times ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Nasara: Gwarazan sojojin Najeriya sun ragargaji yan bindiga a Kaduna, sun ceto mutane

Kebbi: Rayuka 15 ne suka salwanta a farmakin ƴan ta'adda, Jami'ai
Kebbi: Rayuka 15 ne suka salwanta a farmakin ƴan ta'adda, Jami'ai. Hoto daga thecable.ng
Asali: UGC

Mai magana da yawun ƴan sandan ya karyata rahotannin da wasu kafafen watsa labarai ke cewa mutane 50 ne suka rasa rayukansu lokacin aukuwar al'amarin.

Abubakar, wanda ya tabbatar da hakan ga Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya (NAN), yace, "Al'amarin ya auku ne a ranar Juma'a misalin ƙarfe 3:00 na yamma."

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Yace waɗanda ake zargi da zama ƴan bingidan, sun zo ne daga Zamfara, inda suka zagaye yankin kuma suka kai farmaki ga mutane da jami'an tsaro.

"Yayin da labari ya riski hukumar ƴan sanda, hukumar ta turo da ƴan sandan rangadi ƙauyen inda su ka yi bata kashin da ta yi sanadin halakar rayukan ɗan sanda 1 da sojoji 2.
"Mutane 13 suka rasa rayukansu, bayan mun hallaka ƴan bindigan da ba a san yawan su ba yayin musayar wutan."

Kara karanta wannan

Karin Bayani: Yan bindiga sun Hallaka dandazon mutane sun kona wasu a wani mummunan harin Kebbi

Abubakar ya ƙara da bayyana yadda ƴan bindigan suka banka wa wasu gidaje wuta.

Ya ce ana bincika al'amarin, sannan ya na kira ga al'umma baki ɗaya da su ba wa hukumar tsaro haɗin kan da ya dace don ganin an cafke ƴan bindigan.

Jami'in hulda da jama'an ƴan sandan ya ce ƴan sanda tare da goyon bayan mutanen gari, za su ƙara tsauraran matakai don kiyaye maimaita aukuwar ire-iren waɗannan hare-haren.

Ana fuskantar ƙalubalen kashe-kashe da garkuwa da mutane daga ƴan bindiga a Kebbi da wasu jihohin arewa maso yammacin Najeriya.

A shekarar data gabata, anyi garkuwa da sama da dalibai 100 daga makarantar sakandiri a Yauri, inda wasu daga cikine aka saka kwanannan bayan sunyi watanni a hannun 'yan bindigan.

Innalilahi: Yan bindiga sun halaka mutum sama da 30, sun kona kauyuka a jihar Neja

A wani labari na daban, a wani hari mai kama da ɗaukar fansa, yan bindiga sun farmaki ƙauyuka biyu a jihar Neja, sun kashe mutum 37, kamar yadda Punch ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Tashin Hankali: Yan bindiga sun yi mummunar ɓarna a babbar Sakateriyar jam'iyyar PDP

Makonni kalilan da suka shude, wasu Mafarauta da yan Bijilanti suka kashe dandazon yan bindiga, waɗan da ake zargin sun hana zaman lafiya a kauyukan.

Yan ta'addan sun ƙaddamar da mummunan nufin su kan kauyukan Nakuna da kuma Wurukuchi lokacin da mutanen kauyen ke gona.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Khalid avatar

Aisha Khalid (Hausa editor) Aisha Khalid marubuciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018. Ta kwashe shekaru tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu. Za a iya tuntubar ta a adireshin email din ta kamar haka: aisha.khaleed@corp.legit.ng