Da dumi-dumi: Daga dawowa hutu, yan majalisar dattawa sun shiga ganawar sirri
- Majalisar dattawa ta dawo daga hutun Kirsimeti da sabuwar shekara da ta tafi a yau Talata, 18 ga watan Janairu
- Shugaban majalisar dattawa, Ahmad Lawan na isa kan kujerarsa, sai majalisar ta rushe zaman sannan ta shiga labule
- Zuwa yanzu dai babu cikakken bayani game da abun da suke tattaunawa, amma ana ganin batun gyara dokar zabe zai kasance a ciki
Abuja - Bayan tafiya hutun Kirsimeti da na sabuwar shekara, majalisar dattawa ta dawo zama a ranar Talata, 18 ga watan Janairu.
Jaridar The Nation ta rahoto cewa majalisar ta rushe zaman sannan ta shiga ganawar sirri jim kadan bayan shugaban majalisar dattawan, Ahmad Lawan ya dare kan kujerarsa da misalin karfe 10:46 na safe.
Ahmad bayan ya bude taron da addu’a sai ya fada ma shugaban masu rinjaye a majalisar, Sanata Yahaya Abdullahi, da ya yunkura don ganawar sirrin, rahoton Thisday.
Sai dai kuma zuwa yanzu ba a san batutuwan da sanatocin ke tattaunawa akai ba amma ana ganin cewa batun gyaran dokar zabe na 2010 na iya kasance daya daga cikin su.
Shugaban kasa Muhammadu Buhari dai ya ki amincewa da dokar gyaran zaben wanda majalisa ta gabatar masa a shekarar 2021.
Buhari ya bayyana tursasawa jam'iyyun siyasa amfani da tsarin zaben fidda gwani na kai tsaye wajen fitar da yan takararsu a matsayin babban dalilin da yasa yaki amincewa da dokar wacce majalisar tarayya ta aiwatar.
Wasu ‘yan takara za su fuskanci matsala a 2023, ana neman gyara dokar shiga takara
A wani labarin, mun ji cewa yayin da ake shirin zaben 2023, shugaban majalisar wakilan tarayya, Femi Gbajabiamila ya ce akwai bukatar a gyara dokar tsayawa takara a Najeriya.
Jaridar Daily Trust ta fitar da rahoto a ranar Talata, 18 ga watan Junairu, 2022 cewa Rt. Hon. Femi Gbajabiamila yana so a canza sharadin neman shugaban kasa.
Rt. Hon. Gbajabiamila ya yi jawabi na musamman a laccar yaye dalibai da aka yi a jami’ar UNILAG, inda ya bijiro da maganar samun shugabanni masu ilmi.
Asali: Legit.ng