Da Dumi-Dumi: Kun aika duk wanda ya yi yunkurin fasa gidan yari Lahira, Minista ga Jami'ai
- Ministan harkokin cikin gida, Mista Rauf Aregbesola, yace kaiwa gidajen Yari hari tamkar kaiwa ƙasa Najeriya baki ɗaya hari ne
- Minsitan ya umarci jami'an tsaron gidan gyaran hali su bindige duk wanda ya yi yunkurin kai hari a inda ko shurawa ba zai yi ba
- Ya kuma yaba wa jami'an waɗan da aka fi sani da ganduroba kan kokarin su na kare lafiyar fursunoni
Ibadan - Ministan harkokin cikin gida, Rauf Aregbesola, ranar Litinin, ya umarci jami'an tsaron gidan Yari su bindige kowaye ya yi yunƙurin fasa gidan gyaran hali a ƙasar nan.
Punch tace Ministan ya bada wannan umarni ne yayin da ya kai ziyarar duba gidan Yari dake Agodi, Ibadan, babban birnin jihar Oyo.
Yace ya kamata jami'ai su ƙara matsa kaimi wajen tsare gidajen Yari, domin maida shi abu mai wahala wani ya fasa shi.
Ministan ya bayyana cewa duk wani hari da aka kaiwa gidan Gyaran Hali tamkar ƙasar Najeriya ce aka kaiwa hari, kuma ba za'a sake barin haka ta sake faruwa nan gaba ba.
Ku kashe duk wanda ya kawo hari - Aregbesola
A cewar Mista Rauf Aregbesola, kai hari gidajen Yari tamkar ƙunar baƙin wake ne, dan haka duk mai hannu a haka bai dace ya rayu ba bare ya bada labari.
A jawabinsa yace:
"Babban abin da ya fi komai muhimmanci shine tsaron wannan gidan. Ku tsare shi yadda babu wanda ya isa ya fasa shi ko ya farmake shi."
"Wuri ne mai hatsari, duk wanda ya yi yunkurin tada yamutsi sunan shi matacce. Bai kamata ya rayu ba bare ma ya bada labari. Mutane ya kamata su bada labarin sheke shi."
"Ba zamu lamaurci duk wani yunkurin fasa gidajen gyaran Hali ba, kada ku harbi mutum dan ku jikkata shi ko tsorata shi, ku harbe shi a inda zai tafi lahira."
Gwamnati zata kula da walwalar gandirobobi
Ministan ya kuma yaba gandurobobi bisa namijin kokarin da suke yi, kuma ya tabbatar musu da cewa gwamnati zata yi iyakar bakin kokarinta wurin kula da walwala da jin daɗin su.
"Zamu yi bakin kokari wajen kyautata muku domin ku yi aiki tukuru. Wajibi mu yaba muku kasancewar har yanzun babu wani fursuna da aka samu ya harbu da korona."
A wani labarin kuma Mun kawo muku bayanan da ya kamata ku sani game da filin yakin Mbormi, wurin da tsohon sarkin Musulmai Attahiru ya yi shahada a kokarin kare Masarautar Sheikh Bin Fodio
Sheikh Usman Ɗan Fodio, babban malami ne da musulmai ba zasu mance da jihadinsa ba a Najeriya har ya kafa masarautar Musulmai a Sokoto.
Sai dai Khalifa na 12 bayan rasuwar Ɗan Fodio, Sultan Attahiru. ya rasa rayuwarsa ne a kokarin kare martabar Masarautar kakansa.
Asali: Legit.ng