Wata sabuwa: Bashin da ake bin Najeriya ya kara mummunan tashi a 'yan watanni
- Rahoton da muka samo ya bayyana cewa, bashin da ake bin Najeriya na kara hauhawa sama yadda ba a tsammani
- A cikin kasa da watanni 11, an samu karuwar bashin da ake bin kasar zuwa adadin wasu tiriliyoyin Nairori
- A bangaren gwamnati, ministar kudi ta kare wannan bashi, sai dai, masana sun caccaki hakan inda suka ce hadari ne ga kasar
Abuja - Jimillar bashin da ake bin Najeriya ya tashi daga N32.9tn a watan Disambar 2020 zuwa N39.6tn a watan Nuwamba 2021, inji rahoton jaridar Punch.
Ministar kudi, Misis Zainab Ahmed, a yayin gabatar da kasafin kudin shekarar 2022, ta bayyana cewa gwamnati ta ciyo bashin N6.7tn tsakanin watan Janairu zuwa Nuwamba 2021, kamar yadda kwafin gabatarwar ta bayyana.
Sabon rancen ya kunshi bashin gida N5.1tn da kuma N1.6tn da lokuta daban-daban. Sai dai bashin cikin gida ya hada da karbar rance daga babban bankin Najeriya kamar yadda takardar gabatar ta nuna.
A watan Maris na 2021, Ofishin kula da basussuka ya bayyana cewa jimillar bashin da ake bin kasar ya kai N32.9tn a watan Disamba 2020.
Karin rancen N6.7tn na nufin jimillar bashin ya kai kusan N39.6tn a watan Nuwamba 2021.
Hukumar ta DMO ta bayyana cewa basusukan da ake bin kasar nan ya karu zuwa N33.1tn a karshen kwata na farko na 2021, daga N32.9tn a watan Disamba 2020, wanda ya nuna karin kusan biliyan 200.
A cikin kwata na biyu na 2021, jimlar bashin ya tashi da N2.4tn zuwa N35.5tn a watan Yuni 2021.
Kudin ya ci gaba da karuwa da N2.5tn zuwa N38tn zuwa kwata na uku na 2021, wanda shine adadi na karshe da DMO ta bayar.
Duk da haka, bisa bayanin da ministar ta gabatar, an samu karin N1.6tn daga watan Satumba zuwa Nuwamba 2021.
Jaridar Punch din ta kuma ruwaito cewa, a cikin watanni 11, biyan basussukan ya lakume N4.2tn wanda ke daukar 76.2% cikin 100% na kudaden shiga da aka samu na N5.51tn a lokacin.
Ministar ta kare rancen da gwamnati ke karba da kuma bashin da ake bin kasar, tana mai jaddada cewa kasar na da kalubalen kudaden shiga ba wai matsalar basussuka ba, ta kara da cewa har yanzu matakin basussukan yana kan turbar da za a iya biya.
Martanin masana tattalin arziki
Sai dai, masana tattalin arziki da suka hada da tsohon mataimakin gwamnan babban bankin Najeriya da kuma tsohon dan takarar shugaban kasa, Kingsley Moghalu, sun caccaki kare batun basussukan da ministar tayi.
Moghalu ya ce:
“Akwai hanyoyi da yawa da za mu iya bi don inganta yanayin kudaden shiga na cikin gida na Najeriya ba tare da sayar da makomar kasarmu ba.
"Dangane da hujjar cewa Najeriya ba ta da matsalar basussuka sai dai matsalar kudaden shiga, wannan kawai labari ne. Idan kana kashe kobo 90 na kowane Naira daya da ka samu wajen biyan bashi, kana cikin damuwa.
"Ba za ku iya cewa muna da daidaiton bashi da GDP ba wanda zai ba ku damar ci gaba da karbo rance. A'a! Wannan hujja ce ga kasashe masu dorewar tattalin arziki. Ba za ku iya kwatanta Najeriya da kasashe masu ci gaban tattalin arziki ba. Muna cikin tattalin arzikin da har yanzu yana ta tasowa ne.
“Idan ba kwa samun isassun kudaden shiga, me ya sa kuke karbar rance? Kuna kawai kara dagula lamura ne. Me ya sa ba ku mai da hankali kan inda za ku sami kudaden shiga ba maimakon zama cikin kasala da yin watsi da matsalar kuma ku dogara da rance?
“Idan mutum yana rayuwa a haka, zai zama bala’i. Don haka ne ma Najeriya ta fada cikin mawuyacin hali a yau a fannin tattalin arziki.”
A baya-bayan nan ne Bankin Duniya ya ce bashin da ake bin Najeriya na da hadari kuma ya yi yawa.
A wani labarin daban, Babban bankin Najeriya CBN ya fara barazanar amfani da yan sanda wajen damke manoman da suka ki biyan bashin da suka karba karkashin shirin Anchor Borrowers Programme(ABP).
A 2015, Gwamnati ta baiwa manoman shinkafa da wasu tsirrai kudade don inganta aikin noma a Najeriya.
CBN yace ba zai cigaba da lamuntan abinda manoman ke yi na ganin kyauta aka basu kuma kuma duk wanda bai biya ba zai shiga komar hukuma.
Asali: Legit.ng