Zaman lafiya ya samu: Gwamna Buni ya yabawa Buhari bisa magance rashin tsaro a Arewa

Zaman lafiya ya samu: Gwamna Buni ya yabawa Buhari bisa magance rashin tsaro a Arewa

  • Gwamnan jihar Yobe, Mai Mala Buni ya bayyana godiyarsa ga shugaban kasa Muhammadu Buhari na Najeriya
  • Ya bayyana cewa, shugaban ya yi iya kokarinsa wajen tabbatar da zaman lafiya a kasar nan musamman Arewa
  • Hakazalika, ya yabawa shugaban majalisar dattawa, Ahmed Lawan bisa ba gwamnatin Buhari goyon bayan da ake bukata

Gwamnan jihar Yobe, Mai Mala Buni, ya yaba wa shugaban kasa Muhammadu Buhari bisa namijin kokarin da yake yi na maido da zaman lafiya da zaman lafiya musamman a yankin Arewa maso Gabashin kasar nan da ke fama da rikici.

Buni, wanda kuma shi ne shugaban kwamitin riko na jam’iyyar APC mai mulki, ya yi jawabi ne jiya a karshen taron al’adun gargajiya na shekara ta 2022 da aka shafe tsawon mako guda ana yi a Michina, Yobe, This Day ta rahoto.

Kara karanta wannan

Najeriya za ta yi nasara a yaki da rashin tsaro - Tinubu

Gwamnan jihar Yobe ya yabawa Buhari
Gwamna Buni ya yabawa Buhari bisa magance rashin tsaro a Arewa | Hoto: leadership.ng
Asali: Facebook

Ya kara da cewa, an samu ci gaba sosai a harkar tsaro a yankin Arewa maso Gabas, musamman Yobe, inda ya kara da cewa dimbin jama’a da suka halarci bikin al’adun na nuna zaman lafiya ya inganta.

Gwamnan ya kuma godewa Buhari kan yadda ya samar da jami’an tsaro da kuma abubuwan da ake bukata domin tabbatar da tsaron rayuka da dukiyoyi a kasar nan.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Buni ya kuma yabawa Shugaban Majalisar Dattawa, Dakta Ahmad Lawan, bisa yadda ya samar da shugabanci na gari a Majalisar Dokoki ta kasa da kuma bayar da goyon baya da hadin kai da ake bukata domin baiwa bangaren zartaswar gwamnati damar gudanar da ayyukansu.

Ya godewa shugaban majalisar dattawan da ya jagoranci bangaren majalisar, wanda ya ba da hadin kai da goyon bayan da ake bukata ga bangaren zartarwa don aiwatar da aikin da aka dora wa al’umma.

Kara karanta wannan

Yan Najeriya su rika yi mana adalci kan lamarin tsaro, muna kokari:Shugaba Buhari

Buni ya ce ayyuka daban-daban da gwamnati ta aiwatar ko kuma take aiwatarwa a halin yanzu sun samu ne sakamakon hadin kai da goyon baya wanda a baya gwamnatin Buhari ba ta samu ba a shekaru hudun farko.

The Gazette News ta rahoto Buni yana cewa:

“A baya na amince da Ahmad Lawan a matsayin Sardaunan Bade. Ba Sardaunan Bade kadai ba, Sardaunan Arewacin Najeriya ne.
“A nan aka zabe shi a matsayin Sanata saboda wannan mazabarsa ce. Amma Allah Ya sanya shi Shugaban Majalisar Dattawan ta Tarayyar Najeriya.
“Tun da ya hau kujerar shugaban majalisar dattawa, goyon baya da hadin kan da yake baiwa bangaren zartarwa na gwamnati karkashin jagorancin shugaban kasa Muhammadu Buhari ya kawo ci gaba a kasar nan da muke gani a yau.

Jigon APC ya yaba da aikin Buni, ya ba da shawara kan shirin zaben 2023 ga Buhari

A wani labarin, jigon jam'iyyar APC, Hon. Patrick Obahiagbon ya shawarci shugaba Buhari da shugaban kwamitin shirya taron gangamin APC Mai Mala Buni kan shirya hanya dodar ga zaben 2023.

Kara karanta wannan

Tuna baya: Wata 2 da suka gabata, Fashola yace Tinubu zai bayyana burinsa a watan Janairu

Hon Obahiagbon, wanda tsohon dan majalisar wakilai ne ya yi wannan batu ne a ranar Litinin a Abuja, a wata wasikar yabo ga Mai Mala Buni, Daily Trust ta rahoto.

Tsohon dan majalisar ya kara da cewa kada muradin kashin kai da son kai su wuce muradun jam’iyyar.

Hakazalika, ya koka kan yadda jam'iyyar ke fuskantar barazana da rikice-rikicen cikin gida, lamarin da yace ya kamata a kawo karshensa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.