FG ta rantsar da kwamitin zartarwa na hukumar yaki da rashawa, EFCC
- A ranar Alhamis, gwamnatin tarayya ta rantsar da mutum 23 na kwamitin zartarwa na hukumar yaki da rashawa, EFCC
- An samu rahotanni a kan yadda dama tun watan Oktoban shekarar da ta gabata majalisar dattawa ta tabbatar da nadin nasu
- Kakakin EFCC, Wilson Uwujaren, ya ce sakataren gwamnatin tarayya, Boss Mustapha ya yi nadin a madadin gwamnatin tarayya a Abuja
FCT, Abuja - Gwamnatin tarayya a ranar Alhamis ta rantsar da mutum 23 na kwamitin zartarwa na hukumar yaki da rashawa ta EFCC.
Premium Times ta ruwaito yadda tun watan Oktoban shekarar da ta gabata majalisar dattawa ta tabbatar da nadin.
Kakakin hukumar EFCC, Wilson Uwujaren, ya ce sakataren gwamnatin tarayya, Boss Mustapha, ya aiwatar da rantsarwar a madadin gwamnatin tarayya a Abuja ranar Alhamis.
Takardar ta kwatanta bikin rantsarwar a matsayin takaitacce, Premium Times ta ruwaito.
Baya ga shugaban hukumar, Abdulrasheed Bawa, akwai sauran sabbin mambobin kwamitin da aka nada sun hada da: George Ekpungu, sakataren hukumar, Luqman Mohammed, Anumba Adaeze, Kola Adeshina da Yahaya Mohammed. Sauran duk wadanda su ka wakilci hukumomin tsaro da kiyaye dokoki ne.
Shekaru biyar a ke yi a kwamitin
Mr Mustapha ya taya sabbin mambobin murna a kan nadin da aka yi musu, inda ya ce shugaban kasa Muhammadu Buhari ya yaba da nagartar su, kwazon su da kuma jajircewar su wurin taimaka wa hukumar.
Ya yi kira gare su a kan samar tsarika da salo na musamman da zai taimaka wa mulkin shugaban kasa Buhari wurin yaki da rashawa.
“Ana bukatar ku jajirce wurin yaki da rashawa a kasar nan. An ba hukumar damar bincike, gurfanarwa da kuma mika masu laifin da aka kama da rashawa da kuma yaki da ta’addanci.
“Don haka mu na bukatar ku yi amfani da dabarun ku wurin taimakon wannan gwamnati wurin samun nasarar yaki a kan rashawar da ta ke taba tattalin arzikin Najeriya,” a cewarsa.
Cikakken bayani: EFCC ta kwato N152bn da $386m daga mahandama a 2021
A wani labari na daban, hukumar yaki da rashawa ta EFCC, ta samu nasarar amso naira biliyan 152.09 da dala miliyan 386.22 daga mahandama da masu wawura daban-daban a shekarar 2021.
Wilson Uwujaren, shugaban yada labaran EFCC ne ya bayyana hakan ta wata takarda wacce ya saki a Port Harcourt ranar Litinin, Daily Nigerian ta ruwaito.
Daily Nigerian ta ruwaito cewa, hukumar ta yaki da rashawa ta ce ta amso £1.182 miliyan Pounds da 1.723 miliyan na Saudi Riyal cikin shekarar.
Asali: Legit.ng